Majalisar dinkin Duniya ta aika jiragen leken asiri zuwa Kongo
Shirin zaman lafiya na Majalisar dinkin Duniya a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ya fara aika jiragen leken asiri marasa matuka domin sanya ido kan ayyukan ’yan tawaye a kusa da dazukan kan iyaka da kasashen Rwanda da Uganda.Wannan shi ne karo na farko a tarihi da Majalisar dinkin Duniya ta yi amfani da jirage masu leken […]
Shirin zaman lafiya na Majalisar dinkin Duniya a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ya fara aika jiragen leken asiri marasa matuka domin sanya ido kan ayyukan ’yan tawaye a kusa da dazukan kan iyaka da kasashen Rwanda da Uganda.
Wannan shi ne karo na farko a tarihi da Majalisar dinkin Duniya ta yi amfani da jirage masu leken asiri a wani aikinta na zaman lafiya.
An kaddamar da fara amfani da jiragen leken asiri biyu ne daga gabashin birnin Goma, wanda a bara ’yan tawayen M23 suka kama shin a wani karamin lokaci.
Dakarun Malaisar dinkin Duniya a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo sun taka rawa a watan jiya wajen fatattakar ’yan tawayen M23, sai dai sauran masu dauke da makamai suna ci gaba da ayyukansu a kasar.
Wakilin Rediyon BBC a gabashin kasar ta Kongo, Maud Jullien ya ce an dade ana zargin cewa kungiyoyin ’yan tawaye da dama a Arewacin Kibu suna samun makamai ne daga kasashen makwabta.
Sai dai Rwanda da Uganda sun sha musanta zargin cewa suna goyon bayan ’yan tawwayen M23, wadanda a kwanakin baya aka murkushe su da taimakon dakarun zaman lafiya na Majalisar dinkin Duniya dubu 22, wadanda su ne sojiji mafi yawa a duniya da ta taba turawa.
Babban jami’in tabbatar da zaman lafiya na Majalisar dinkin Duniya, Herbe Ladsous ya shaida wa BBC cewa jiragen leken asiri ko “jirage marasa makamai ko matuka” za su kasance zabi mafi dacewa domin sanya ido kan ayyukan masu dauke da makamai da kuma kai-kawon fararen hula. “Muna bukatar sanin cikakken abin da ke gudana,” inji shi.
Ya ce idan aka samu nasarar haka a Dimokuradiyyar Kongo, za a iya amfani da su a sauran ayyukan zaman lafiya na Majalisar dinkin Duniya.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ce jiragen leken asirin biyu na farko wani kamfanin kasar Italiya mai suna Seled ES, wanda bangare na wani babban kamfanin Italiya mai suna Finmeccanica, ya kera su. Kuma jami’an majalisar sun ce ana sa ran kara aikawa da jiragen leken asirin guda uku a watanni masu zuwa. Kuma za a tura su yankunan Arewacin Kibu mai albarkatun kasa da yakin na shekara 20 ya fi yi wa illa a kasar.
Ministan tsaro na Kongo, Aledandre Luba Ntambo ya ce jiragen leken asirin za su taimaka wa sojojin kasar a kan ’yan tawayen. “Idan muka san hakikanin wurin da suke boye, za mu fi aiwatar da ayyukanmu,” inji shi.
Duk da fatattakar ’yan tawayen M23, wasu kungiyoyin masu dauke da makamai suna ci gaba da kai-kawo a gabashin Kongo ciki har da kungiyar FDLR da aka zargi shugabanninta da hannu a kisan kare-dangi na Rwanda a 1994.