Majalisar dinkin Duniya ta amshe aikin samar da zaman lafiya a kasar Mali

Kwamitin Tsaro na Majalisar dinkin Duniya (UNSC) ya amince a tura sojojin kawo zaman lafiya dubu 12 da 600 zuwa kasar Mali. Sojojin za su fuskanci kalubalen da kasar ke fama da kuma tsabagen zafin turirin sahara.A yanzu dai sojojin kasashen Afirka ne ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar inda suka mayye gurbin […]

Majalisar dinkin Duniya ta amshe aikin samar da zaman lafiya a kasar Mali
Majalisar dinkin Duniya ta amshe aikin samar da zaman lafiya a kasar Mali

Kwamitin Tsaro na Majalisar dinkin Duniya (UNSC) ya amince a tura sojojin kawo zaman lafiya dubu 12 da 600 zuwa kasar Mali. Sojojin za su fuskanci kalubalen da kasar ke fama da kuma tsabagen zafin turirin sahara.
A yanzu dai sojojin kasashen Afirka ne ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar inda suka mayye gurbin sojojin kasar Faransa da suke janyewa bayan kai farmakin soja ga maboyar ’yan tawayen kasar. Sai dai duk da haka Faransa za ta bar sojojina dubu daya a kasar.
A ranar Talatar da ta gabata ce Kwamitin Tsaron ya amince ya karbi aikin wanzar da zaman lafiyar ba tare da hamayya ba, kuma za a “canja hular kwano” daga koriya da sojojin Afirka ke amfani da ita zuwa shudiya ta Majalisar dinkin Duniya.
Ana sa ran a gudanar da zabe a kasar Mali a ranar 28 ga Yuli, kuma sojan Majalisar dinkin Duniyar za su fara kula da kasar daga farkon watan gobe.
Za a kira rundunar da sunan MINUSMA wato Rundunar Daidaita Al’amura a Mali kuma za ta dauki nauyin ayyukan da suka hada da tsaro da daidaita al’amura da sanya ido kan hakkin dan Adam da kare fararen hula tare da tsarawa da gudanar da zabe mai inganci cikin kwanciyyar hankali a kasar Mali.