Majalisar dinkin Duniya ta bayyana maboyar madugun ’yan tawayen Uganda
Wani rahotan kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya ya ce madugun mayakan kungiyar ’yan tawayen Uganda ta LRA wato Joseph Kony ya na buya ne a wani yanki da ke kasar Sudan ta Kudu wanda ke makwabtaka da kasar Sudan da kuma Jamhuriyyar Tsakiyar Afrika. An dade ana neman Mista Kony ruwa-a-jallo saboda tuhumarsa da […]
Wani rahotan kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya ya ce madugun mayakan kungiyar ’yan tawayen Uganda ta LRA wato Joseph Kony ya na buya ne a wani yanki da ke kasar Sudan ta Kudu wanda ke makwabtaka da kasar Sudan da kuma Jamhuriyyar Tsakiyar Afrika.
An dade ana neman Mista Kony ruwa-a-jallo saboda tuhumarsa da ake a Kotun Manyan Laiffuka bisa laifukan yaki da fyade da kuma tilasta wa yara kanana shiga aikin soja. Jagoran ’yan tawayen dai ya kaddamar da yaki kan gwamnatin Uganda tun kimanin shekara 20 kenan. kungiyarsa ta LRA ta sha yunkurin hanbarar da gwamnatin Shugaba Yoweri Musebeni ba tare da samun nasara ba. Kuma jagororinta kab tilasta wa duk wanda ya shiga hannunsu shiga kungiyar, idan kuma ya ki, sai su datse wasu daga cikin sassan jikinsa nan take.
Bayan dakarun Uganda sun fatattakesu daga kasar nan ne, ’yan tawayen suka bulla kasashe makwabta ciki har da Jamhuriyar Damukradiyyar Kongo.