Majalisar dinkin Duniya ta janye sojojinta daga Dimokuradiyyar Kongo

Majalisar dinkin Duniya ta janye sojojinta daga gabashin Dimokuradiyya Kongo sakamakon rashin korar wadansu janar biyu na kasar da gwamnatin kasar ta yi.Mai magana da yawun majalisar Nick Birnback ne ya shaida wa BBC shekaranjiya Laraba, inda ya ce wadannan sojojin sun aikata laifuffukan da suka keta hakkin dan Adam ba tare da an hukunta […]

Majalisar dinkin Duniya ta janye sojojinta daga Dimokuradiyyar Kongo
Majalisar dinkin Duniya ta janye sojojinta daga Dimokuradiyyar Kongo

Majalisar dinkin Duniya ta janye sojojinta daga gabashin Dimokuradiyya Kongo sakamakon rashin korar wadansu janar biyu na kasar da gwamnatin kasar ta yi.
Mai magana da yawun majalisar Nick Birnback ne ya shaida wa BBC shekaranjiya Laraba, inda ya ce wadannan sojojin sun aikata laifuffukan da suka keta hakkin dan Adam ba tare da an hukunta su ba.
A yanzu sojojin majalisar dinkin duniya ba za su shiga cikin sojojin gwamnatin kasar da ke fafatawa da ’yan tawaye ba, saboda zargin su da keta hakkin dan Adam.
Tun a farko an shirya yadda za a kwace makaman da ke hannun ’yan tawayen kasar da ake kira FDLR, wadanda suka kasance barazana ga zaman lafiya a kasar.
Har zuwa yanzu gwamnatin kasar ba ta ce komai a kai ba.
A baya dai an rawaito cewa gwamnatin kasar ta riga ta zabi sojojin da za su yaki ’yan tawayen FDLR, kuma sun ce ba za karbi umarni daga majalisar dinkin duniya ba.
daya daga cikin sojojin da suke jagorantar yaki da ’yan tawayen mai suna Janar Bruno Mandebu, yana cikin jerin sunayen sojojin da suke da bakar lamba a wurin majalisar dinkin duniya, inda take zarginsa da aikata laifuffuka 121 ciki har da fyade da daukar doka a hannunsa.
Sai dai gwamnatin kasar ta ce ba shi da laifi face sai an tabbatar da akasin hakan.