Majalisar dinkin Duniya ta yaba wa Kamaru

Babban jami’in Majalisar dinkin Duniya mai kula da ‘yan Gudun Hijira Antonio Guterres ya yaba wa hukumomin kasar Kamaru saboda yadda suka bai wa ’yan gudun hijirar Najeriya mafaka. Jami’in ya bayyana hakan ne lokacin wata ziyara da ya kai sansanin ‘yan gudun hijira na garin Minawao a lardin Arewa mai nisa na kasar Kamaru […]

Majalisar dinkin Duniya ta yaba wa Kamaru
Majalisar dinkin Duniya ta yaba wa Kamaru

Babban jami’in Majalisar dinkin Duniya mai kula da ‘yan Gudun Hijira Antonio Guterres ya yaba wa hukumomin kasar Kamaru saboda yadda suka bai wa ’yan gudun hijirar Najeriya mafaka.

Jami’in ya bayyana hakan ne lokacin wata ziyara da ya kai sansanin ‘yan gudun hijira na garin Minawao a lardin Arewa mai nisa na kasar Kamaru shekaranjiya Laraba ,inda tarin ‘yan gudun hijira na kasar Najeriya suke zaune bayan sun guje wa hare-haren ’yan kungiyar Boko Haram.
Babban jami’in ya gana wa idanunshi ne halin da ’yan gudun hijiran suke rayuwar da suke ciki da kuma irin bukatun da suke da su wurin ci gaba da rayuwa. A hirar da wakilinmu yi da wasu, sun shaida wa Aminiya cewa babbar matsalarsu ita ce na samun tsaftaceccen ruwan sha da isasshen abinci duk da cewa kuma ana dinga ba su abincin lokaci-lokaci bisa ga wa’adin da aka diba, amma kuma abincin na kare wa gabannin haka.
Wata bukatar da ’yan gudun hijira suke da ita ita ce na rashin isasshen makewayi a dalilin haka ya sa tari daga cikinsu suka maida wasu wurare, inda suke biyan bukatunsu. Hakan kuma na da hadari ga lafiyarsu. A ganawar da Antonio Guterres ya fara yi da wasu manyan jami’an gwamnati a nan birnin Yaounde kamar Sakataren Fadar Shugaban kasa da kuma ministan harkokin waje ya yaba wa Kamaru wadda ya ce ta bude iyakokinta domin ba wa ‘yan gudun hijira shigowa, sa’annan kuma ta ba su mafaka da kuma tsaro.