Majalisar Dinkin Duniya ta yi alla-wadai da harin Bama
Majalisar Dinkin Duniya ta yi alla-wadai da wani harin da ’yan ta’adda suka kai a garin Darul Jamal, da ke karamar hukumar Bama a Jihar Borno.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi alla-wadai da wani harin da ’yan ta’adda suka kai a garin Darul Jamal, da ke karamar hukumar Bama a Jihar Borno.
Mohamed Malick Fall, Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan jinkai na Majalisar a Nijeriya, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan lamarin, wanda ya faru a yammacin ranar Jumma’a, 5 ga watan Satumba.
“Ina matukar bakin ciki da rahoton kisan da aka yi wa sojoji da fararen hula da dama a ranar Juma’a a kauyen Dara Jamal,” in ji Fall.
Rahotannin farko sun nuna cewa an kashe fararen hula fiye da 50, inda ake zargin an yi garkuwa da wadanda ba a san adadinsu ba.
Kazalika, bayanai sun nuna mutane da dama sun gudu daga muhallansu, sannan an kone gidaje fiye da 20 kurmus a lokacin harin.
Jami’in, a madadin ofishin majalisar a Nijeriya, ya kuma mika saƙon ta’aziyya ga iyalan wadanda harin ya shafa, gwamnati, da kuma al’ummar Jihar Borno, tare da yi wa wadanda suka ji rauni fatan samun sauki cikin gaggawa.
“Ina kira ga hukumomin tsaro da su kamo wadanda suka aikata wannan ɗanyen aikin. Ina kuma kira da a gaggauta sakin duk wadanda aka sace,” in ji shi.
Jami’in ya bayyana lamarin a matsayin wani mummunan tunatarwa kan yadda tashe-tashen hankula da rashin tsaro ke ci gaba da addabar Jihar Borno a duk shekara.
Rahotanni sun nuna cewa, an dade ana kashe fararen hula da ‘yan gudun hijira, manoma, matafiya, da ‘yan kasuwa a irin wadannan hare-haren.
Dabarun da ‘yan ta’adda ke amfani da su sun hada da bama-bamai da kai harin kunar bakin wake, da dai sauran munanan hanyoyi.
Bugu da kari, Fall ya lura cewa jihohin Adamawa da Yobe da ke da makwabtaka da Jihar Borno ba su tsira ba, inda aka kai hare-hare a cibiyoyin kiwon lafiya da kuma kasuwanni.
Majalisar Dinkin Duniya ta sake jaddada aniyar ta na ci gaba da tallafawa wadanda rikici ya shafa a Nijeriya, a kokarin da gwamnatin ke yi na dakile ayyukan ‘yan ta’adda..