Majalisar dinkin Duniya ta yi wa kalaman Donald Trump raddi
Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar dinkin Duniya ta yi gargadin cewa musayar kalaman da ake yi don neman tsaya wa jam’iyyu takarar shugabancin kasar Amurka yana yin illa a kan shirin tsugunar da ’yan gudun hijirar Siriya a kasar Amurka.Mai magana da yawun hukumar ta yi wannan bayani ne a matsayin raddi […]
Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar dinkin Duniya ta yi gargadin cewa musayar kalaman da ake yi don neman tsaya wa jam’iyyu takarar shugabancin kasar Amurka yana yin illa a kan shirin tsugunar da ’yan gudun hijirar Siriya a kasar Amurka.
Mai magana da yawun hukumar ta yi wannan bayani ne a matsayin raddi ga kalaman daya daga cikin masu son yin takarar shugabancin kasar a karkashin Jam’iyyar Republican, Donald Trump wanda a ranar Litinin ya yi kira a hana Musulmi shiga kasar kwata-kwata.
Ta ce irin wadanan kalamai da gwamnonin jihohin Amurka da dama suka yi na sanya abin da ta kira muhimmin shirin sake tsugunar da ’yan gudun hijira a tsaka-mai-wuya.
Kalaman Mista Trump sun janyo suka sosai daga duk bangarorin siyasar kasar. Kodayake, ya ce yana nan a kan bakarsa.
Sai dai daraktan majalisar da ke hada kan Musulmi Amurkawa, Nihad Awad, ya shaida wa BBC cewa Donald Trump mutum ne da ke da hadari ga zaman lafiya kuma kalamansa sun fi kama da na “wani shugaban ’yan daba.”