Majalisar dinkin Duniya ta zargi Isra’ila da aikata laifukan yaki
A shekaranjiya Laraba ne Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Majalisar dinkin Duniya ta kira wani taron gaggawa wanda bayan kammala shi, ta zargi kasar Isra’ila da aikata laifukan yaki.Kwamishinan Hukumar Nabi Pillay ya bayyana cewa akwai zarge-zargen aikata laifufan yaki a rikicin da ke faruwa a zirin Gaza kuma za su fara binciken a […]
A shekaranjiya Laraba ne Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Majalisar dinkin Duniya ta kira wani taron gaggawa wanda bayan kammala shi, ta zargi kasar Isra’ila da aikata laifukan yaki.
Kwamishinan Hukumar Nabi Pillay ya bayyana cewa akwai zarge-zargen aikata laifufan yaki a rikicin da ke faruwa a zirin Gaza kuma za su fara binciken a kan hakan. Har ila yau, a shafin zumuntarsa na intanet ya bayyana damuwa game da farmakin da Isra’ila take kai wa Falasdinawa.
Amma a lokacin taron da aka gudanar a birnin Geneba, Jakadan Isra’ila Ebiatar Manor ya zargi hukumar da gazawa wajen kare Yahudawa. Ya ce jama’ar Gaza ba abokan gabar Isra’ila ba ne kuma kasar Isra’ila, kasa ce mai mutunta dokokin kasa-da-kasa. A karshe jakadan ya zargi hukumar da rura wutar rikicin.
Kodayake Ministan Harkokin Wajen Falasdinu Riad al- Malki ya yi kira ga manyan kasashen duniya da su shiga tsakani. Ya ce, “Isra’ila na ci gaba da aikata manyan laifukan yaki. Tana kashe iyalai saboda haka ya zama wajibi ta fuskanci hukunci. ” inji shi.
Bugu da kari, Falasdinawa da wasu kasashen Larabawa sun shigar da wani daftari a gaban hukumar inda suka bukaci ta binciki zargin da ake wa Isra’ila na aikata laifukan yakin da kuma sabawa dokokin kasa-da-kasa. Amma daftarin bai ambaci kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ba.
Tun da farko Isra’ila ta so membobin kasashen hukumar su hana taron wakana, amma sai Falasdinawan suka samu goyon bayan galibinsu.