Majalisar dinkin Duniya ta zargi Koriya ta Arewa da tallafa wa Syriya da makamai masu guba
A wani rahoto na musamman da Majalisar dinkin Duniya ta bayyana, ya nuna cewa Koriya ta Arewa na aikawa Syria wasu abubuwa da a ke amfani da su wajen sarrafa makaman nukiliya ta jiragen ruwa. Rahoton da masana a Majalisar ta dinkin Duniya su ka rubuta, wanda kuma jaridu da dama su ka gani, ya […]

A wani rahoto na musamman da Majalisar dinkin Duniya ta bayyana, ya nuna cewa Koriya ta Arewa na aikawa Syria wasu abubuwa da a ke amfani da su wajen sarrafa makaman nukiliya ta jiragen ruwa.
Rahoton da masana a Majalisar ta dinkin Duniya su ka rubuta, wanda kuma jaridu da dama su ka gani, ya ce abubuwan da a ke zargin kasar ta Koriya ta Arewa suna aika wa kasar Syria sun hada da tayil-tayil da wanda asid ba ya iya bata su da na’urorin auna yanayi wato thermometer.
Haka kuma, rahoton ya ce an sha ganin wasu ma’aikatan Koriya ta Arewa su na aiki a wuraren sarrafa makamai a cikin Syria.
Gwamnatin Syria dai ta yadda a rushe ma’adanar sinadaran kemical dinta bayan wani harin gas din Sarin da ya kashe daruruwan mutane a Ghout a shekarar 2013, amma ko bayan nan an tuhume ta da kai hare-haren da ake tunanin ta yi amfani da sinadaran na masu guba kamar yadda BBC ta ruwaito.
Rahoton ya ce a baya an shigar da irin wadannan kaya sau 40 tsakanin shekarar 2012 zuwa ta 2017.
Wannan zargi dai ya biyo bayan sabon rahoton da aka samu cewa dakarun Syria su na amfani da makamai masu guba, duk da cewa gwamnatin kasar ta yi watsi da wannan zargi.
Sai dai an yi ta jin karar hare-haren sama a yankin Gabashin Ghouta da ke wajen birnin Damascus bayan da aka shiga kwana biyu na dakatar da fadan da ake yi don a samu damar shigar da kayan agaji.
Masu fafutuka dai suna zargin hare-haren kasa da na sama da gwamnati ke kai wa ya hana a shigar da kayan agaji ga fararen hula, yayin da Rasha kuma ke zargin ‘yan tawaye.
kasashen duniya dai sun kakaba wa Koriya ta Arewa takunkumai kan shirinta na makami mai linzami.
Amma wani rahoton sirri da wata tawagar kwararru na Amurka ta hada wanda BBC ta gani, wanda ya yi duba kan yadda Koriya ta Arewa ke yin biyayya ga dokokin Majalisar dinkin Duniy, ya gano cewa ta karya dokoki wajen aikewa da kayayyakin zuwa kasar Syria.
An yi zargin cewa wata cibiyar kimiyya ta Gwamnatin Syria SSRC ce ta biya Koriya ta Arewa kudaden kayan ta hannun wasu kamfanoni.
Gwamnatin Syria na tallafawa cibiyar SSRC a matsayin cibiyar bincike ta farar hula, amma Amurka ta zargi cibiyar da mayar da hankali kan hada makamai masu guba.