Majalisar Dokokin Amurka ta gayyaci dan Donald Trump
‘Yan majalisar Dokokin Amurka sun nemi dan g Shugaban kasar, Donald Trump Junior da ya bayyana a gabansu kan batun mallakar bayanan batanci ga abokiyar takarar mahaifinsa, Hillary Clinton kamar yadda BBC ta ruwaito. Donald Trump Junior dai ya ce bai yi wa mahaifinsa magana ba kan haduwa da wata lauya ‘yar kasar Rasha wadda […]

| ‘Yan majalisar Dokokin Amurka sun nemi dan g Shugaban kasar, Donald Trump Junior da ya bayyana a gabansu kan batun mallakar bayanan batanci ga abokiyar takarar mahaifinsa, Hillary Clinton kamar yadda BBC ta ruwaito. |
Donald Trump Junior dai ya ce bai yi wa mahaifinsa magana ba kan haduwa da wata lauya ‘yar kasar Rasha wadda ta nemi ta tallafa wa yakin gangamin zaben Trump, da bayanan batanci ga Hillary Clinton, a bara.
Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Chuck Schumer ya nemi dan shugaban tare da wasu manyan jami’an gwamnatin kasar da su bayyana a gabansu domin su yi gamsasshen bayani.
A wata hira da gidan talbijin na Fod News, Donald Trump Junior ya bayyana haduwa da lauyar da wani abun da bai kai ya kawo ba.
Ya ce “idan na waiwayi al’amarin ina ganin ya kamata in yi wani abu daban da hakan. Kuma wannan dai wani shaci-fadin jaridun Rasha ne kawai amma ba abun da haduwar tamu ta tattauna a kai ba ke nan.”
Sai dai kuma da farko Trump Junior ya saki wasu jerin sakonni imail da ke nuna yadda ya yi maraba da bukatar haduwa da lauyar ‘yan kasar ta Rasha.
Manyan ‘yan majalisar Dokokin Amurkar dai sun bayyana bayanan da ke cikin sakonni imail din da Trump Junior ya saki da abun takaici.
Yanzu haka dai ana ganin kokarin da gwamnatin Trump ta yi na nesanta kanta da Rasha yana neman ya zama yaudara.