Majalisar Dokokin Filato ta kori dukkan Ciyamomin Jihar
’Yan majalisar sun dauki matakin ne yayin zamansu ranar Alhamis
Mambobin Majalisar Dokokin Jihar Filato sun kori dukkan Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar su 17 daga kan kujerunsu.
’Yan majalisar sun dauki matakin ne yayin zamansu ranar Alhamis, wanda Kakakin majalisar, Abok Ayuba, ya jagoranta.
- Ba za mu yi zanga-zanga kan cire tallafin mai ba – ’Yan kwadago
- Shugaba Tinubu ya yi ganawar farko da shugabannin tsaro
Hakan dai ya biyo bayan amincewa da wani kuduri da dan majalisa mai wakiltar Langtang ta Arewa, Pirfa Tyem.
Ya ce an kawo kudurin ne bayan wata kara da kuma bukatar haka da Gwamnan Jihar, Caleb Mutfwang, da ya yi wa shugabannin da yin rub da ciki a kan dukiyar Kananan Hukumomin.
Ayuba, wanda ya sanar da dakatarwar bayan an amince da kudurin, ya kuma bukacin Ciyamomin da su mika ragamar mulki da duk wani kayan gwamnati da ke hannunsu ga Daraktocin Mulki na Kananan Hukumominsu, yayin da za a fara bincike.