Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta zabi shugabanninta

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Alhaji Ibrahim Balarabe Mohammed ya bukaci mambobin majalisar su ba sababbin shugabannin majalisar cikakken goyon baya don su samu damar gudanar da shugabancinsu yadda ya kamata.Shugaban ya yi wannan kira ne jim kadan bayan zaben shugabannin da ya gudana a zauren majalisar da ke Lafiya. Ya ce kowa a cikin […]

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta zabi shugabanninta
Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta zabi shugabanninta

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Alhaji Ibrahim Balarabe Mohammed ya bukaci mambobin majalisar su ba sababbin shugabannin majalisar cikakken goyon baya don su samu damar gudanar da shugabancinsu yadda ya kamata.
Shugaban ya yi wannan kira ne jim kadan bayan zaben shugabannin da ya gudana a zauren majalisar da ke Lafiya. Ya ce kowa a cikin mambobin majalisar na da amfani kuma dukkansu daya ne, inda ya shawarci wadanda aka zaba su dauki zabensu a matsayin wata dama ce ta bayar da gudamawarsu don cigaban majalisar da jihar baki daya.
Shugaban ya kuma bayyana cewa kasancewar majalisar tana da muhimmanci kuma aikin kirkiro da dokoki da ke inganta rayuwar al’ummar jihar ya rataya a wuyanta ne dole shugabannin su tabbatar suna gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon amana ba tare da nuna son kai ba don ci gaban jihar.
Sababbin shugabannin majalisar da Jam’iyyar APC ke da rinjaye, sun hada da Umar Tunga daga mazabar Arewacin Awe a matsayin Shugaban Masu Rinjaye sai Ogbere Kana daga mazabar Kokona ta Kudu a matsayin Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye. Sai Makpa Mala daga mazabar Wamba a matsayin Babban Mai Tsawatarwa da Dogara James daga Doma ta Kudu, Mataimakin Babban Mai Tsawatarwa.
A jawabansu na godiya wadanda aka zabar sun yi alkawarin gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon amana. Kuma sun gode wa takwarorinsu da suka zabe su inda suka tabbatar musu cewa ba za su ba su kunya ba. Sun bukaci su ba su hadin kai domin kai majalisar da jihar baki daya ga tudun mun tsira.
Majalisar ta gayyaci shugabannin hukumomin tsaro a jihar su bayyana a gabanta don su bayyana mata yanayin tsaro a fadin jihar baki daya.

Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi 

Amarya ta yanke maƙogwaron ango a Kano

NAJERIYA A YAU: Masu nau’in jinin AS sun fi masu AA lafiya — Masana

ADC za ta ƙalubalanci hukuncin soke mata rajista