Majalisar Dokokin Kaduna ta buƙaci a binciki El-Rufa’i

Kwamitin ya ce akwai buƙatar gurfanar fa El-Rufai don yin bincike a kansa.

Majalisar Dokokin Kaduna ta buƙaci a binciki El-Rufa’i

Kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, da ya binciki zargin almundahana da badakalar kudi a lokacin gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya mika rahotonsa ga majalisar.

Shugaban kwamitin wucin gadin, Henry Zacharia ne, ya gabatar da rahoton yayin zaman majalisar na ranar Laraba.

Kwamitin wanda aka dora wa alhakin binciken bashi, tallafi, da wasu kwangiloli da gwamnatin El-Rufai ta yi daga shekarar 2015 zuwa 2023, ya bayyana cewa ba a yi amfani da bashin yadda ya dace ba.

Rahoton kwamitin ya zargi tsohon gwamna El-Rufai da ‘yan majalisarsa da laifin badakala, bayar da kwangiloli ba bisa ka’ida ba, da kuma karkatar da kudaden jama’a.

Kwamitin ya ce basussukan da El-Rufai ya karbo sun wuce ƙima, wanda hakan ya jefa Kaduna cikin ƙangin bashi.

Da yake karbar rahoton, kakakin majalisar dokokin Kaduna, Yusuf Liman, ya bayyana cewa gwamnatin El-Rufai ta karkatar da Naira biliyan 423.

Kwamitin ya bayar da shawarar gudanar da bincike tare da gurfanar da El-Rufai da sauran jami’an gwamnatinsa.

Rahoton ya buƙaci a gaggauta dakatar da kwamishinan kudi na Jihar Kaduna, Shizer Badda da shugaban hukumar kula da ilimin bai ɗaya na jihar, waɗanda suka yi aiki a gwamnatin El-Rufai.

Kazalika, kwamitin ya kuma buƙaci a gudanar da bincike kan wasu da suka taɓa riƙe manyan muƙamai a gwamnatin El-Rufai.

Aminiya ta ruwaito yadda Gwamna Ubah Sani, ya ce gwamnatinsa na fuskantar ƙalubale wajen biyan albashi a jihar, sakamakon ɗimbin bashin da ya gada daga uban gidansa.

Gwamnan, ya ce gwamnatin ta gaji bashin dala miliyan 587 da Naira biliyan 85, da kuma bashin kwangila 115 daga gwamnatin El-Rufai.

Sani, ya koka kan yadda farashin canjin dala ya ƙara yawan bashin da gwamnatin baya ta karɓo.

{ "statusCode": 500, "error": { "type": "SERVER_ERROR", "description": "An error while processing your request. Please try again later." } }