Majalisar dokokin Kano na tantance sabon mataimakin Gwamnan jihar
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa sunan Garo ga majalisar ne a ranar Talata domin tabbatar da shi, biyo bayan murabus ɗin tsohon mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo.
Manyan jami’an jam’iyyar APC a jihar Kano, ciki har da Ministar Jiha ta Abuja (FCT), Mariya Mahmud, sun raka sabon wanda aka zaɓa a matsayin Mataimakin Gwamna, Murtala Sule Garo zuwa majalisar dokokin jihar domin gudanar da tantancewa a ranar Alhamis.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa sunan Garo ga majalisar ne a ranar Talata domin tabbatar da shi, biyo bayan murabus ɗin tsohon mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo.
- Sojoji sun daƙile harin Boko Haram da kashe ’yan ta’adda
- DSS ta gurfanar da El-Rufai kan zargin yin kutse a wayar Ribadu
A ranar Laraba kuma, majalisar ta kafa kwamitin da zai tantance sabon wanda aka zaɓa.
Sauran manyan jami’an da suka raka Garo zuwa kwamitin majalisar sun haɗa da Shugaban kwamitin kasafi na majalisar wakilai, Abubakar Kabir Bichi, da ɗan majalisa Alhassan Ado Doguwa, da ɗan majalisa Sagir Ibrahim Koki da kuma tsohon Minista, Abdullahi Tijjani Gwarzo da dai sauransu.
