Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da Shugaban Karamar Hukuma
An dakatar da shi ne tsawon wata uku saboda badakalar filaye
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Gwale da ke Jihar, Khalid Ishaq Diso, na tsawon wata uku.
Hakan dai ya biyo bayan amincewa da rahoton kwamitinta na kananan hukumomi da masarautu, a zamanta na ranar Talata.
- Mutanen da girgizar kasa ta yi wa ajali a Morocco sun zarta 2,800
- Kotu ta kwace kujerar Sanata da dan majalisar PDP a Filato
Ana dai zargin Shugaban Karamar Hukumar ne da badakalar sayar da filayen gwamnati da kuma yanke hukunci ba tare da tuntuba ba.
Majalisar ta kuma ce 6 daga cikin Kansilolin Karamar Hukumar su 10 ne suka kai karar Ciyaman din a kan ayyukansa da ba su lamunta ba.
Kakakin Majalisar, Jibril Isma’il Falgore, ya kuma ce an zargi Ciyaman din da yin komai shi kadai ba tare da saurarar Kansiloli ba.
Majalisar ta kuma kafa kwamitin wucin gadi domin ya binciki zarge-zargen sannan ya kai mata rahoto cikin wata biyu.
Ta kuma bukaci Mataimakin Ciyaman din ya karbi ragamar Karamar Hukumar a tsawon watanni ukun har sai an kammala binciken.