Majalisar Dokokin Katsina ta rage kasafin kudin 2020

A yau Alhamis  Gwamnan Jahar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya rattabawa kasafin kudin shekarar 2020 hannu, a gidan gwamnati bayan amincewar Majalisar Dokokin Jihar. Kasafin kudin wanda Gwamna Masari ya gabatarwa Majalisar a cikin watan Nuwanbar 2019, na sama da Naira biliyan 249 majalisar ta rage shi zuwa Naira bilyan 244 bayan tantancewar  da […]

Majalisar Dokokin Katsina ta rage kasafin kudin 2020

Gwamna Masari a gaban Majalisar Dokokin jihar

A yau Alhamis  Gwamnan Jahar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya rattabawa kasafin kudin shekarar 2020 hannu, a gidan gwamnati bayan amincewar Majalisar Dokokin Jihar.

Kasafin kudin wanda Gwamna Masari ya gabatarwa Majalisar a cikin watan Nuwanbar 2019, na sama da Naira biliyan 249 majalisar ta rage shi zuwa Naira bilyan 244 bayan tantancewar  da majalisar tayi.

A lokacin da yake sanyawa kasafin kudin hannu, Gwamna Masari ya ce, zasu tabbatar da cewa sun kammala aiyukan da aka faro ba’a kammala. Kazalika, gwamnati zata inganta bangaren aiyuka na musamman da sashen kasafin kudin da tsare-tsare ta hanyar yin taro da jama’a yadda zasu fahimci muhimmancin shi kasafin kudin da ake yi.

Gwamna Masari, ya ce, “Zamu fara yin wannan taro na dandalin saduwa da jama’a kai tsaye a cikin zango na uku na wannan shekara. Shirin kuma zamu yi shi ne a matakin shiyya wadda zamu karkasa shiyyar zuwa wasu bangarori ta yadda za’a ba jama’a damar sanin abin da ke faruwa.”