Majalisar Faransa ta amince da kafa kasar Falasdinu
A ranar Talatar da ta gabata ne Majalisar Dokokin kasar Faransa ta amince da kafa kasar Falasdinu da gagarumin rinjaye. A lokacin zaman ’yan majalisar su 339 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudirin, yayin da 151 suka yi adawa da matakin. Kuma ana kallon kuri’ar za ta taimaka wajen matsa wa gwamnatin Faransa lamba […]
A ranar Talatar da ta gabata ne Majalisar Dokokin kasar Faransa ta amince da kafa kasar Falasdinu da gagarumin rinjaye.
A lokacin zaman ’yan majalisar su 339 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudirin, yayin da 151 suka yi adawa da matakin. Kuma ana kallon kuri’ar za ta taimaka wajen matsa wa gwamnatin Faransa lamba kan fara zartar da matakin.
Wani jagora a kungiyar kwato ’yancin Falasdinawa ta (PLO) Hanan Ashrawi ya ce suna godiya ga mambobin majalisar Faransa saboda daukar wannan mataki mai adalci da daraja hakkin dan Adam da suka yi. Faransa dai ta dade tana bayyan goyon bayanta ga kafa kasar Falasdinu.
kudirin da jam’iyya mai mulki ta Socialists ta gabatar, ya bukaci gwamnatin Faransa ta amince da kasar Falasdinu wajen magance rikicin Gabas-ta-Tsakiya. Kuma ana ganin matakin ba zai yi wa kasar Isra’ila dadi ba, musamman ganin yadda kasashen Spain da Birtaniya da kuma Sweden suka amince da kafa kasar Falasdinawan.