Majalisar Gombe ta ki tantance Kwamishinoni kwana 38 da karbar sunayensu

“Hakan na da nasaba da takun saka tsakanin majalisar da bangaren zartarwa”

Majalisar Gombe ta ki tantance Kwamishinoni kwana 38 da karbar sunayensu

Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya

Majalisar Dokokin Jihar Gombe ta ki tantance sunayen mutum 17 da Gwamna Inuwa Yahaya ya aike mata don nadawa Kwamishinoni kwanaki 38 da suka gabata.

Aminiya ta rawaito cewa Gwamnan ya aike wa majalisar da sunayen ne ranar 28 ga watan Yuli, kwana 60 ke nan bayan an rantsar da shi, kamar yadda doka ta tanada.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ne dai ya mika sunayen ga Akawun majalisar, Rukaiyatu A. Jalo, kuma daga bisani Kakakin majalisar, Abubakar Mohammed Leggerewo, ya karanta su a zauren majalisar.

Daga cikin mutum 17 din dai, shida sun taba rike matsayin a wa’adin farko na Gwamnan, yayin da 11 kuma sababbi ne.

Wakilinmu ya gano cewa jim kadan bayan bayyana sunayen Kwamishinonin, ’yan majalisar sun sanar da tafiya hutun mako uku, inda suka shirya dawowa ranar 21 ga watan Agusta.

To sai dai kimanin mako biyu bayan cikar wa’adin dawowar ’yan majalisar, har yanzu sun ki zama su tantance Kwamishinonin.

Wani ma’aikacin majalisar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce hakan ba ya rasa nasaba da takun sakar da ke tsakanin bangaren zartarwa da na majalisar a kan wasu kudaden alawus-alawus dinsu.

Ya ce ko a makon da ya gabata sai da ’yan majalisar suka zauna da nufin magance matsalar da kuma tantance sunayen.

Sai dai a cewar Daraktan Yada Labarai na majalisar, Abubakar Mohammed Umar, sai ranar Talata ’yan majalisar za su dawo daga hutun nasu.

Ya ba da tabbacin cewa da zarar sun dawo, za su fara aikin tantance mutanen.