Majalisar Jihar Bauchi ta kwanta da sirdi
Abin da muka dade muna fadi kan yadda Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta zama ’yar amshin Shata, ya kara tabbata, inda abin da muke gudu ya faru da ita, ta kasance a rufe wata da watanni. Mun yi ta kokarin janyo hankalin wakilan majalisar kan yadda suka zama bi-ta-zaizai ga bangaren zartarwa na jihar, wanda […]
Abin da muka dade muna fadi kan yadda Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta zama ’yar amshin Shata, ya kara tabbata, inda abin da muke gudu ya faru da ita, ta kasance a rufe wata da watanni.
Mun yi ta kokarin janyo hankalin wakilan majalisar kan yadda suka zama bi-ta-zaizai ga bangaren zartarwa na jihar, wanda yake juya su yadda ya so kamar waina, amma sai aka dauka ba mu kaunar majalisar ce ko gwamnatin jihar.
Sanannen abu ne cewa wakilci nagari a kowace majalisa ba yana nufin adawa da bangaren zartarwa ba ne, a’a majalisa tamkar linzami take ga bangaren zartarwa, idan ta ga yana neman wuce gona da iri ta yi dakatar da shi, idan kuma yana tafiyar hawainiya ya yi masa kaimi.
Kowannenmu yana sane cewa al’amuran gwamnati a Jihar Bauchi ba su tafiya yadda suka kamata, wasu ayyuka da aka faro kusan shekara hudu da suka gabata suna nan tamkar jiya aka fara. Sannan wasu ayyukan da suka bijiro saboda wasu lalurori wasu ma ko waiwayarsu ba a yi ba, balle a gyara. Misali ayyukan ginin hanyoyi da gwamnatin ta faro watannin farko na hawanta karaga akwai hanyar da ta tashi daga shataletalen Sakatariyar Jiha ta wuce Kofar Wase, wannan hanya ko daya bisa 10 ba a kammala ba, kai wadansu ma suna cewa da gwamnatin ta bar ta yadda ta same ta da ya fi. Haka aikin fadada titunan shiga Bauchi daga Jos duk da cewa aikin tarayya ne amma ana zargin gwamnatin jihar ta yi kane-kane ta hana aikin gudana, baya ga tsuke hanyar da aka yi daga ainihin yadda take a baya. Wadda ta tashi daga shataletalen otel din Awalah aka ce za ta kai Kwalejin Giwo an ki karasa ta da kimanin kilomita daya, haka na Kofar Gombe zuwa Inkil. Wasu matsalolin da suka taso su ne na kwarewar rufin makarantu da asibitoci da sauran gine-ginen gwamnati da na jama’a. Gwamnatin ta gaza gyara akasarin nata gine-ginen, balle ta tallafa wa jama’ar da suka rasa muhallansu a guguwar da ta faru washegarin Karamar Sallah a birnin Bauchi da kewaye.
Gwamnatin Bauchi kusan ta kare ne a kan batun biyan albashi kadai, ayyukan ci gaba ba a ta tasu, domin wasu ayyukan ma ko kananan hukumomi suke yi yanzu ya kamata a ce an gama su, amma shiru muke ji.
Majalisa wadda ita ya kamata ta rika sa ido kan shiga da fitar kudin jihar ta koma wani muhalli na maula da kamun kafa da cin dunduniyar juna. Wannan ne ya jawo wakilan majalisar ba su farga ba, sai da kaikayi ya koma kan mashekiya aka yi waje da su a zaben fid-da-gwani na APC.
Bayanai suna nuna cewa rashin nasara a zaben fid-da- gwani da wakilan majalisar da dama suka iske kansu a ciki, ya sa sun fara shirin tsige shugaban majalisar Alhaji Kawuwa Shehu Damina daga kujerarsa, kuma akwai rade-radin bayan sun cire shi, sai su tado da batun tsige Gwamna Mohammed Abubakar daga kujerarsa. Sai dai kuma bangaren zartarwa ya yi musu shigar sauri, inda aka ce gwamnati ta bayar da kwangilar gyara ginin majalisar, lamarin da ya jawo aka rufe majalisar na sai abin da hali ya yi. Yanzu dai babu wanda zai ce yaushe za a bude majalisar, kuma ko da an bude ta ina lokacin da za a yi wani abin kirki yake?
Don haka wannan fargar Jaji ce suka yi, wadda ba ta da wani amfani. Abin da kawai za su yi a sauran watannin da suka rage musu, shi ne su kokarta su tabbatar da ana aiwatarwa da kammala dukan ayyukan da aka faro a jihar.
Ga al’ummar Jihar Bauchi kuma ina kira gare su cewa, a zabe na gaba su tsaya su zabi mutane masu gaskiya da rikon amana masu kishin jihar ba masu kwadayin tara abin duniya ba. Idan haka ta samu ne za mu samu wakilai nagari da za su yi wa jihar aiki bisa adalci tare da tsare amanar dukiyar al’umma.
Alhaji Gambo Abdullahi Bababa
Shi ne Shugaban Kungiyar Masu Sarrafa Magungunan Gargajiya ta Jihar Bauchi, za a iya samunsa ta tarho: 08023622651 da 07032096837