Majalisar Jihar Ekiti ta amince da karin kasafin Biliyan 10 na Fayose

Majalisar Jihar Ekiti ta amince da karin kasafin kudi na Naira biliyan 10 cikin awa daya kacal bayan Gwamnan Jihar Ayodele Fayose ya aike musu da bukatar hakan kwanaki kadan kafin ya tattara inasa-inasa ya bar ofishin gwamnan. A cikin awa da zaman, wanda aka farad a misalin karfe 12 na rana, an karanta kudurin […]

Majalisar Jihar Ekiti ta amince da karin kasafin Biliyan 10 na Fayose
Majalisar Jihar Ekiti ta amince da karin kasafin Biliyan 10 na Fayose

Majalisar Jihar Ekiti ta amince da karin kasafin kudi na Naira biliyan 10 cikin awa daya kacal bayan Gwamnan Jihar Ayodele Fayose ya aike musu da bukatar hakan kwanaki kadan kafin ya tattara inasa-inasa ya bar ofishin gwamnan.

A cikin awa da zaman, wanda aka farad a misalin karfe 12 na rana, an karanta kudurin na farko da na biyu, sannan kwamitin kasafin kudi ya duba, kuma aka tabbatar.