Majalisar jihar Kano kafa kwamitin binciken bidiyon Ganduje
Majalisar dokokin jihar Kano ta kaddamar da kwamiti na mutum bakwai domin yin bincike a kan wasu jerin bidiyo da ke ikirarin nuna gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da karbar ‘cin hanci’ daga wajen wasu ‘yan kwangila. Daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar daga mazabar Warawa Labaran Madari ne ya bukaci majalisar da […]
Majalisar dokokin jihar Kano ta kaddamar da kwamiti na mutum bakwai domin yin bincike a kan wasu jerin bidiyo da ke ikirarin nuna gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da karbar ‘cin hanci’ daga wajen wasu ‘yan kwangila.
Daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar daga mazabar Warawa Labaran Madari ne ya bukaci majalisar da ta binciki sahihanci bidiyon da ake ta yadawa game da Gwamnan.
Shugaban masu rinjaye a majalisar Baffa Babba Dan-Agundi ne zai jagoranci kwamitin da aka kafa.
Mambobin kwamitin sun hada da: Labaran Madari, mai tsawatarwa na majalisar Zubairu Massu da Garba Ya’u Gwarmai da Abdulaziz Garba Gafasa da Abubakar Uba Galadima, yayin da Mujitaba Aminu zai zama sakataren kwamitin
Kakakin majalisar jihar Kabiru Rurum ya bukaci kwamitin da su kammala binciken rahoton a cikin wata daya.