Majalisar jihar Kano ta amince da nada Kwamishinoni 4

Majalisar dokokin jihar Kano a yau Laraba ta amince da sunayen sababbin Kwamishinoni 4 da Gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje ya tura wa zauren majalisar. Kakakin majalisar dokokin jihar Alhaji Kabiru Rurum ya ce, majalisar ta karbi wasikar da Gwamna Ganduje ya aikawa majalisar a ranar 27 ga Disamba 2018 don tantance sunayen da amincewar zauren […]

Majalisar jihar Kano ta amince da nada Kwamishinoni 4

Majalisar dokokin jihar Kano a yau Laraba ta amince da sunayen sababbin Kwamishinoni 4 da Gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje ya tura wa zauren majalisar.

Kakakin majalisar dokokin jihar Alhaji Kabiru Rurum ya ce, majalisar ta karbi wasikar da Gwamna Ganduje ya aikawa majalisar a ranar 27 ga Disamba 2018 don tantance sunayen da amincewar zauren majalisar.

‘Yan majalisar sun amince da sunayen sababbin Kwamishinonin bayan kwamitin tantancewa ya mika rahotansa.

Kwamishinonin sun hada da: Malam Bashir Yahaya-Karaye da Alhaji Mukhtar Ishak-Yakasai da Alhaji Shehu Kura da kuma Alhaji Muhammad Tahir wanda aka fi sani da Baba Impossible.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta