Majalisar jihar Katsina ta yi sabon kakaki
A yau Litinin dan majalisar dokokin jihar Katsina daga mazabar Zango, Tasi’u Musa Maigari ya zama kakakin majalisar jihar. An dai zabi Maigari ne a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar bayan yin murabus din tsohon kakakin majalisar Abubakar Yahaya Kusada wanda a yanzu yake neman takarar majalisar wakilan tarayya daga mazabun Ingawa da Kusada da […]
Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari
A yau Litinin dan majalisar dokokin jihar Katsina daga mazabar Zango, Tasi’u Musa Maigari ya zama kakakin majalisar jihar.
An dai zabi Maigari ne a matsayin kakakin majalisar dokokin jihar bayan yin murabus din tsohon kakakin majalisar Abubakar Yahaya Kusada wanda a yanzu yake neman takarar majalisar wakilan tarayya daga mazabun Ingawa da Kusada da kuma Kankiya.
Sabon kakakin ya dage zaman majalisar zuwa ranar 14 ga Janairu 2019.