Majalisar Jihar Nasarawa ta kafa kwamiti kan tsaro
Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta kafa wani kwamiti da ya kunshi dukkan shugabannin majalisar don yin la’akari da yanayin tsaro a jihar. Kafa kwamitin ya biyo bayan wani kudiri ne da wakilin mazabar Nasarawa-Eggon ta Gabas, Muhammed Agah Muluku ya shigar dangane da sace tsohuwar Shugabar Marasa Rinjaye ta Majalisar Misis Mary Enwongulu da ’yan […]
Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta kafa wani kwamiti da ya kunshi dukkan shugabannin majalisar don yin la’akari da yanayin tsaro a jihar.
Kafa kwamitin ya biyo bayan wani kudiri ne da wakilin mazabar Nasarawa-Eggon ta Gabas, Muhammed Agah Muluku ya shigar dangane da sace tsohuwar Shugabar Marasa Rinjaye ta Majalisar Misis Mary Enwongulu da ’yan bindiga suka yi kwanakin baya, wadda aka sako ta bayan iyalanta sun biya wasu kudi da ba a bayyana adadinsu ba.
Kwamitin har wa yau zai duba batun fashi da makami da ke aukuwa a kai-a kai a wurare da dama na jihar don samar da hanyoyin magance su.
A jawabinsa jim kadan bayan kaddamar da kwamitin Shugaban Majalisar Alhaji Balarabe Ibrahim Muhammed ya ce ya zame wa gwamnatin jihar dole ta yi dukkan mai yiwuwa don ganin ta kare ’yan siyasa da sauran al’ummarta baki daya daga sharrin miyagun mutane.
Ya bayyana garkuwa da Mary Enwongulu da ’yan bindiga suka yi a matsayin abin fargaba duk da cewa an sako ta, inda ya ce hakan babu shakka ya nuna cewa rayuwar ’yan siyasa a jihar tana cikin hadari.
Ya ce a kan haka ne majalisar ta ga ya dace ta kafa wannan kwamiti cikin gaggawa don dakile ayukan wadannan batagari.
Shi ma wakilin mazabar Akwanga ta Kudu, Kasim Kasim ya ce yanayin rashin tsaro a karamar Hukumar Akwanga ya zame abin damuwa matuka da a cewarsa ke bukatar mafita cikin gaggawa. Saboda haka ya yi kira ga bangarorin tsaro a jihar su inganta yanayin tsaro a jihar, kuma kada su yi wata-wata wajen hada hannu da gwamnati don kawo karshen lamarin.
Idan za a iya tunawa a kwanakin baya ne wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka sace Mary Enwongulu a gidanta da ke garin Akwanga inda a makon da ya gabata suka sako ta bayan iyalanta sun biya wasu makudan kudd da ba a bayyana adadinsu ba.