Majalisar Jihar Sakkwato ta fara binciken Gwamnatin Wamakko

Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta fara bincikar tsohuwar gwamnatin Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko inda ta gayyaci Babban Ma’ajin Kudi na Jihar Alhaji Aminu Abdullahi da Babban Mai Bincike na Jihar Alhaji Sambo Nawawi don sanin al’amuran kudin gwamnatin da ta gabata a wannan shekara.Majalisar tana bukatar samun bayanan kudin da gwamnatin Wamakko ta karbo ko […]

Majalisar Jihar Sakkwato ta fara binciken Gwamnatin Wamakko
Majalisar Jihar Sakkwato ta fara binciken Gwamnatin Wamakko

Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta fara bincikar tsohuwar gwamnatin Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko inda ta gayyaci Babban Ma’ajin Kudi na Jihar Alhaji Aminu Abdullahi da Babban Mai Bincike na Jihar Alhaji Sambo Nawawi don sanin al’amuran kudin gwamnatin da ta gabata a wannan shekara.
Majalisar tana bukatar samun bayanan kudin da gwamnatin Wamakko ta karbo ko ta batar don haka ta umarci jami’an su ba ta bayyani dalla-dalla tun daga watan Junairu zuwa Agustan bana.
Bayan doguwar tattaunawar da aka yi tsakanin kwamitin sanya ido kan dukiyar jama’a da yaki da rashawa na majalisar da jami’an gwamnati an cimma matsayar za a kawo wa majalisar a yau Juma’a. i.  
Shugaban Kwamitin Alhaji Malami Galadanci ya ce binciken zai san duk abuubuwan da jihar ke da su da kudin shigarta da sanin abin da take amfana da shi.
Ya ce, “Muna son sanin ko akwai bashi don samun ci gaban jihar nan, kan haka muke bukatar Babban Ma’ajin Kudi na Jiha ya ba mu dukkan takardun da suka shafi kudi a jihar nan, manuufarmu da yin wannan aikin mu tabbata jama’armu sun samu romon dimokuradiyya da kuma sauke nauyin da aka rataya mana.”
Makonni biyu da suka gabata tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Wammako ya bayyana cewa bai bar wa jihar bashi ba sabanin sauran jihohi da ke da fama da kantar bashi.

Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi 

Amarya ta yanke maƙogwaron ango a Kano

NAJERIYA A YAU: Masu nau’in jinin AS sun fi masu AA lafiya — Masana

ADC za ta ƙalubalanci hukuncin soke mata rajista