Majalisar Kaduna ta binciki Kwamishinonin El-Rufai

Kwamitin ya yi wa wasu Kwamishinoni da suka yi aiki da tsohon Gwamna Nasir El-Rufai tambayoyi.

Majalisar Kaduna ta binciki Kwamishinonin El-Rufai

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta gudanar da binciki wasu tsofaffin kwamishinonin dangane da hada-hadar kuɗi da suka haɗa da lamuni da kwangiloli da gwamnatin jihar ta gudanar a tsakanin ranar 29 ga watan Mayun 2015 zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Kwamitin wucin-gadi da majalisar ta kafa ya yi wa wasu Kwamishinoni da suka yi aiki da tsohon Gwamna Nasir El-Rufai titsiye dangane da yadda suka gudanar da harkokin kuɗi yayin da suke riƙe da akalar jagoranci.

Shugaban kwamitin, Henry Danjuma, ya ce tsofaffin kwamishinonin da aka gayyata sun haɗa da na Ayyuka da Ababen More Rayuwa, Thomas Gyang; Kwamishinan Ilimi, Ja’afaru Ibrahim Sani; Kwamishinan Noma, Dakta Manzo Daniel Maigari; Kwamishinan mulki na birnin Zariya, Balarabe Aliyu; Babban Darakta na Hukumar Kula da Hanyoyin Kaduna (KADRA), Injiniya Mohammed Lawal Magaji; da kuma Shugabar Hukumar Raya Birnin Kafanchan, Phoebe Yayi Sukai.

Da yake zantawa da manema labarai a harabar majalisar, Shugaban Kwamitin ya ce, “Tun lokacin da aka ƙaddamar da kwamitin, muna gudanar da ayyukanmu sosai.

“A yau, mun gayyaci wasu manyan mutane don amsa tambayoyi da ake ganin ya zama dole domin tattara shaidu masu mahimmanci don cimma matsaya mai kyau da kuma bayar da cikakken rahoton binciken.”

Aminiya ta ruwaito cewa, kafa kwamitin ya samo asali ne daga ƙorafe-ƙorafen da Gwamna Uba Sani ya yi kan ƙalubalen da aka samu a Kasafin Kuɗi da ake dangantawa da basussuka da aka ranto a gwamnatin El-Rufai.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos