Majalisar Kaduna ta buƙaci bayanan kashe kuɗaɗe a mulkin El-Rufa’i

Uba Sani ya koka kan yadda tsohon gwamna El-Rufai ya bar wa Jihar Kaduna tarin bashi.

Majalisar Kaduna ta buƙaci bayanan kashe kuɗaɗe a mulkin El-Rufa’i

An buƙaci Ma’aikatar Kuɗi ta Jihar Kaduna da ta gabatar da cikakkun bayanai kan duk wata hada-hadar kuɗi a ƙarƙashin tsohon gwamna Nasir El-Rufai wanda ya mulki Kaduna tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.

Majalisar Dokokin Kaduna ce ta gabatar da buƙatar ne dangane da ci gaba da binciken duk wasu kuɗaɗe, lamuni da ayyukan da aka bayar ƙarƙashin gwamnatin tsohon gwamnan na wa’adi biyu da ya yi.

Ana iya tuna cewa Gwamna Uba Sani ya caccaki magabacinsa, El-Rufa’i kan ɗimbin bashin da ya bar wa ofishinsa.

Gwamna Uba, wanda ya yi magana a yayin wani taro da aka yi a Kaduna, ya koka da yadda ba zai iya biyan albashin ma’aikata ba saboda baitul-malin da ya gada akwai bashi.

Dangane da haka ne Majalisar Dokokin Kaduna ta amince ta binciki gwamnatin El-Rufai, lamarin da ya kai ga ƙaddamar da kwamitin da zai jibinci lamarin.

Magatakardar Majalisar, Sakinatu Idris ce ta rubuta wa Kwamishinan Kuɗi buƙatar duk wasu takardu masu alaƙa da hada-hadar kuɗi tsakanin watan Mayu 2015 zuwa Mayu 2023.

A cikin wasiƙar, majalisar ta umurci ma’aikatar da ta miƙa dukkan bayanan da suka shafi hada-hadar kuɗi ga kwamitin da aka kafa domin binciken duk wasu ayyukan kuɗi, lamuni da kwangila da aka bayar a ƙarƙashin gwamnatin El-Rufai.

Takardar ta bayyana cewa, “An umurce ni da in nemi ku tura wa Kwamitin wucin gadi takaddun da aka jera da duk sauran takardun da kuke ganin sun dace da aikin kwamitin.

“Ana bukatar duk wasu bayanai na lamuni daga watan Mayun 2015 zuwa Mayu 2023 tare da amincewar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna.

“A taron da Majalisar zartaswa ta Jiha ta yi, da abubuwan da majalisar ta fitar da kuma ƙuduri game da lamuni.  Sun haɗa da biyan kuɗaɗe da basukan lamuni ga ‘yan kwangila daga Mayu, 2015 zuwa Mayu, 2023.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta