Majalisar Kaduna ta soke hukumar kula da manyan biranen jihar
Majalisar ta ce ta soke dokar kula da biranen ne bayan hukuncin Kotun Koli na bai wa ƙananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu.
Majalisar Dokokin Kaduna ta rushe dokar da ta kafa hukumar kula da biranen Zariya da Kaduna da kuma Kafanchan.
A ranar Laraba Majalisar ta soke dokar da ta kafa hukumar wacce tsohuwar gwamnatin Nasir El-Rufai ta ƙirƙiro a shekarar 2021.
Majalisar ta ce ta soke dokar kula da biranen ne bayan hukuncin Kotun Koli na bai wa ƙananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu.
“Don haka yanzu babu buƙatar wannan hukumomi” da El-Rufai ya kafa a lokacinsa dake kula da biranen jihar.
- NAJERIYA A YAU: Shin Zanga-Zanga Kan Sauya Al’amura A Najeriya?
- Ba mu janye daga zanga-zangar da za a gudanar ba — NLC
Dama dai dangantaka ta yi tsami a tsakanin tsohon El-Rufai da majalisar dokokin jihar da kuma gwamnan yanzu, Uba Sani.
Zaman doya da manja tsakanin gwamnatin Uba Sani da El-Rufai har ta kai ga majalisar ta kafa kwamitin binciken Gwamnatin El-Rufai daga 2015-2023.
Tsamin dangantakar tasu ta kai ga har El-Rufai ya maka Gwamnati da Majalisar dokokin Jihar bisa tuhumar da suka yi masa na kartatar da Naira biliyan 423.
El-Rufai, wanda ya bayyana zargin a matsayin “neman bata suna” ya maka majalisar dokokin a kotu domin neman haƙƙinsa.
Majalisar ta ce ta soke dokar kula da Biranen ne bayan hukuncin Kotun Koli na bai wa ƙananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu.
“Don haka yanzu babu buƙatar wannan hukumomi” da El-Rufai ya kafa a lokacinsa dake kula da biranen jihar.