Majalisar Kano ta amince wa Abba ya nada masu ba shi shawara 20

Majalisar ta amince da bukatar gwamnan bayan karanta wasikarsa a ranar Laraba.

Majalisar Kano ta amince wa Abba ya nada masu ba shi shawara 20

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da bukatar Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ta neman ya nada masu ba shi shawara na musamman guda 20.

Kakakin Majalisar, Ismail Jibrin Falgore ne, ya karanta wasikar bukatar Gwamnan a zauren majalisar a ranar Laraba.

Aminiya ta rawaito cewa an tattauna wasikar ce kafin majalisar ta amince da bukatar.

Majalisar ta dage zamanta zuwa ranar 19 ga watan Yuni, 2023 a wani kudiri da shugaban masu rinjaye, Honarabul Lawan Husaini (Dala) ya gabatar kuma ya samu goyon bayan shugaban marasa rinjaye, Labaran Abdul Madari (Warawa).

Wannan dai shi ne zama na farko d Majalisar Dokokin jihar ta 10 ta yi bayan rantsar da ita a ranar Talata.

Majalisar dai ta zabi Ismail Jibrin Falgore na jam’iyyar NNPP a matsayin Shugabanta.

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda