Majalisar Kano ta bukaci a cire Babban Akantan Jihar
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci a cire Babban Akantan Jihar, Dokta danjuma Yankatsari daga mukaminsa saboda gazawar bayyana a gabanta domin ya yi mata cikakken bayani kan matsayin kudin jihar.Majalisar ta dauki wannan mataki ne bayan zaman da ta yi, inda Kwamitin Kudi a karkashin jagorancin Alhaji Abubakar Zakari Muhammad ya bukaci a cire […]
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci a cire Babban Akantan Jihar, Dokta danjuma Yankatsari daga mukaminsa saboda gazawar bayyana a gabanta domin ya yi mata cikakken bayani kan matsayin kudin jihar.
Majalisar ta dauki wannan mataki ne bayan zaman da ta yi, inda Kwamitin Kudi a karkashin jagorancin Alhaji Abubakar Zakari Muhammad ya bukaci a cire Akanta Janar din bisa abin da ta kira kin bayyana hakikanin gaskiyar matsayin kudin Jihar Kano a matsayinsa na Babban Akanta.
Ana zargin Babban Akantan sa ne da kin amsa kiran majalisar game da matsayin kudin jihar, lamarin da ya sa ’yan majalisar suka bukaci gwamnatin jihar ta cire shi.
Ya zuwa aiko da wannan labari babu wata sanarwa ko tsokaci da suka fito daga ofishin Babban Akantan.