Majalisar Kano ta dakatar da Shugaban Hukumar Gwale kan sayar da filaye

Majalisar Kano ta dakatar da Khalid Ishaq Diso kan zargin sayar da filayen karamar hukumar da kuma watsi da kansiloli

Majalisar Kano ta dakatar da Shugaban Hukumar Gwale kan sayar da filaye

Majalisar Dokokin jihar Kano

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da Shugaban Hukumar Gwale, Khalid Ishaq Diso na tsawon wata uku kan zargin sayar da filayen karamar hukumar.

A ranar Talata Majalisar ta dakatar da Khalid Ishaq Diso, wanda kuma take zargin ya mayar da kansilolin karamar hukumar saniyar ware.

Majalisar ta sanar da dakatar da Khalid Diso, wanda dan jam’iyyar adawa ta APC ne, bayan da ta karbi rahoton kwamitinta na kananan hukumomi da harkokin masarautu a yayin zaman.

Shugaban majalisar, Jibril Ismail Falgore, ya ce sun samu takardar korafi daga mutun shida cikin kansiloli 10 na Karamar Hukumar Gwale kan  wasu abubuwan da shugaban karamar hukumarsu ke yi da ba su gamsu da su ba.

Jibril Falgore ya ce kansilolin na kuma zargin shugaban karamar hukumar da rashin tafiya tare da su wajen gudanar da harkokin karamar hukumar.

A kan haka ne majalisar ta kafa kwamitin bincike, wanda ta ba wa wa’adin wata biyu ya kawo mata rahotonsa.

Daga nan majalisar ta umarci mataimakin shugaban karamar hukumar ya maye gurbin Diso, zuwa lokacin da za a kammala binciken.

ACF ta yi Allah-wadai da harin Sakkwato, ta nemi a yi bincike

Tinubu ya yaba wa NNPCL kan fara aikin Matatar Warri

Masu son Abba ya tsaya da ƙafarsa za su cuce shi – Kwankwaso

Matatar Warri ta fara aiki bayan shekara 9