Majalisar Kano ta fara binciken zargin tatsar kudade daga dalibai
Ana zargin tatsar kudade daga hannun daliban kwalejin kiwon lafiya ta Kano.
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta fara bincike kan zargin tatsar makudan kudade babu gaira, babu dalili daga hannun daliban Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta Jihar Kano.
Majalisar ta kafa kwamitin binciken zargin yadda ake karbar kudade iri-iri daga hannun daliban kwalejin kiwon lafiyar da sunan kudaden ka’ida ba tare an ba su rasidi ba.
- Daga Laraba: Tsakanin uwa da uba laifin waye lalacewar tarbiyyar ’ya’ya?
- Ganduje ya tura wa majalisa kwarya-kwayar kasafin N33.8bn
Zauren majalisar ya kafa kwamitin ne bayan dan majalisa mai wakiltar Doguwa, Hon. Alhaji Salisu Ibrahim, ya yi korafi a kan lamarin.
Bayan gabatar da korafin tare da neman a binciki lamarin, ya samu goyon bayan Alhaji Nuhu Achika mai wakiltar Wudil.
Daga na Shugaban Majalisar, Hamisu Chidari, ya amince tare da kafa kwamitin binciko gaskiyar lamarin.
Hakan ya faru ne a zama majalisar na ranar Talata inda ta tattauna a kan bukatar gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, na amincewarta da karin Naira biliyan 33.8 a kan kasafin 2021 mai karewa.
Takardar bukatar gwamnan ta ce karin kasafin ya kunshi biliyan N21.5 na manyan ayyuka, biliyan N9.2 na gudanar da ofisoshin gwamnati da kuma biliyan N3.22 na biyan albashi.
ta ce idan aka sanya kwarywa-kwarywar kasafin kudi da aka gabatar a cikin kasafin 2021 na Jihar Kano, jumullarsa zai karu zuwa Naira biliyan 231.7.
A cewar gwamnan, yin karin kasafin ya zama wajibi domin gwamnatin jihar ta samu damar sauke nauyin da ya rataya a wuyanta da kuma kammala manyan ayyuka da ta faro.
Ya ce za a samo kudaden ne daga harajin da gwamnatin jihar take tarawa da kuma wasu hanyoyi da ta bullo da su.
Majalisar ta amince da kudurin domin ci gaba da aiki a kai a zamanta na gaba.