Majalisar Kano ta kafa kwamitin tantance Murtala Garo a matsayin Gataimakin Gwamna

Ana sa ran kwamitin zai gayyaci Garo domin tantance shi, domin gabatar da rahoto ga zauren majalisar a ranar Litinin.

Majalisar Kano ta kafa kwamitin tantance Murtala Garo a matsayin Gataimakin Gwamna

Murtala Sule Garo

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa kwamitin tantance Murtala Sule Garo, a matsayin wanda zai zame sabon mataimakin gwamnan jihar.

Majalisar ta kafa kwamitin ne bayan karanta wasikar da ke dauke da bukatar nadin, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike wa shugabanta, Jibril Ismail Falgore, a zauren majalisar a ranar Laraba.

Gwamnan ya bayyana cewa ya zabi Murtala Sule Garo ne bayan zuzzurfan tattaunawa da tuntaba a fadin jihar, yana mai bayyana Garo a matsayin gogaggen dan siyasa mai kwarewa a fannin shugabanci.

Ya bayyana cewa a baya Garo ya kasance Mashawarcin Gwamna Kan Harokokin Jam’iyyu, Shugaban Karamar Hukumar Kabo, Shugaban Kungiyar Kannan Hukumomi (ALGON) Reshen Jihar Kano, da kuma Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu.

Da yake jaddada bukatar majalisar ta tantance Garo a kan lokaci domin kada a samu gibi a harkar shugabanci, Gwamna Abba ya jaddada kwarin gwiwarsa cewa kwarewar Garo da kuma fahimtarsa ga yanayin siyasar Jihar Kano za su takama muhimmiyar rawa wajen biyan bukatun al’ummar jihar.

Bayan nan ne shugaban majalisar ya kafa kwamitin wucin gadi domin tantancewar karkashin jagoranci Mataimaki Shugaban Majalisar, da Shugaban Masu Rinjaye, Mai Tsawatarwan Majalisar, Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye, da ’yan majalisar masu wakiltar Fagge, Sumaila, Warawa, Dawakin Kudu da Tudun Wada da sauranasu.

Ana sa ran kwamitin zai gayyaci Garo domin tantance shi, domin gabatar da rahoto ga zauren majalisar a ranar Litinin.