Majalisar Kano ta yi wa dokar hukumar tace fina-finai gyaran fuska

Ɗaya daga cikin sabbi gyaran da aka yi mata shi ne na wajabta wa masu wuraren bukukuwa da taruka yin rajista da hukumar.

Majalisar Kano ta yi wa dokar hukumar tace fina-finai gyaran fuska

Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta amince da yi wa dokar da ta kafa Hukumar Tace Fina-finai ta jihar gyare-gyare.

Ɗaya daga cikin sabbi gyaran da aka yi mata shi ne na wajabta wa masu wuraren bukukuwa da taruka yin rajista da hukumar.

Wannan mataki ya zo ne saboda yadda ayyukan hukumar ke jan hankali, inda sau da yawa ake samun saɓani tsakaninta da wasu.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawal Husaini Dala ne, ya bayyana cewa an yi wannan dokar gyara ne don daidaita harkokin ɗaukar fina-finai da kare addini da al’adu.

Ya ce daga yanzu ba wanda zai iya ɗaukar fim a Kano ba tare da izinin hukumar ba.

A nasa ɓangaren, Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Kano, Abba El-Mustapha, ya gargaɗi masu wallafa bidiyo a shafukan sada zumunta da su guji duk wani abu da zai taɓa mutuncin addini, al’adun Hausawa, ko kuma darajar al’ummar Kano.

Ya ce hukumar za ta mara wa masu ƙirƙirar bidiyo na nishaɗi da kasuwanci, amma ba ga waɗanda ke amfani da kafafen sada zumunta don cin mutunci ba.

Haka kuma, El-Mustapha ya bayyana cewa hukumar tana da ikon ɗaukar mataki kan duk wani abu da ya saɓa wa al’adu da addini, musamman idan aka samu ƙorafi.

Yanzu haka dai majalisar dokokin jihar ta kammala nata aikin, saura gwamnan Kano ya sanya hannu a kan dokar domin ta fara aiki.

Sai dai har yanzu ba a tantance lokacin da gwamnan zai rattaɓa hannu a kai ba.