Majalisar kasa ta amince da Naira dubu 27 mafi karancin albashi

Majalisar kasa ta Najeriya ta amince da tsayar da Naira dubu 27 a matsayin karamin albashin ma’aikata a jihohi. Yayin da Majalisar ta kuma amince da Naira dubu 30 a matsayin karamin albashi ga ma’aikatan gwamnatin tarayya. A yau Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar a fadarsa wadda ta kunshi tsofaffin shugabanni […]

Majalisar kasa ta amince da Naira dubu 27 mafi karancin albashi

Majalisar kasa ta Najeriya ta amince da tsayar da Naira dubu 27 a matsayin karamin albashin ma’aikata a jihohi. Yayin da Majalisar ta kuma amince da Naira dubu 30 a matsayin karamin albashi ga ma’aikatan gwamnatin tarayya.

A yau Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar a fadarsa wadda ta kunshi tsofaffin shugabanni da tsofaffin alkalan alkalan Najeriya da kuma gwamnoni da shugabannin majalisa.

Ministan kwadago na Najeriya Chris Ngige ya bayyana cewa, za a mika kudirin ga majalisa a ranar Laraba domin amincewar ta.

 

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta