Majalisar Katsina ta amince a kafa kwalejin noma a Daudawa
Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta amince da kafa Kwalejin Harkokin Noma a garin Daudawa, Karamar Hukumar Faskari. Mataimakin Shugaban Majalisar, Hon. Shehu Dalhatu Tafoki ne ya gabatar da kudurin a zauren majalisar. ASUU ta gindaya wa Gwamnati sharadin janye yajin aiki Yadda Najeriya za ta bunkasa kasuwanci da fasahar zamani — NITDA An sa ranar […]
Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta amince da kafa Kwalejin Harkokin Noma a garin Daudawa, Karamar Hukumar Faskari.
Mataimakin Shugaban Majalisar, Hon. Shehu Dalhatu Tafoki ne ya gabatar da kudurin a zauren majalisar.
- ASUU ta gindaya wa Gwamnati sharadin janye yajin aiki
- Yadda Najeriya za ta bunkasa kasuwanci da fasahar zamani — NITDA
- An sa ranar nadin sarautar sabon Sarkin Zazzau
Yayin gabatar da kudurin, Hon Tafoki mai wakilatar yankin ya ce, “Kuduri ne da ke fatan samar da cikakkiyar kwalejin harkokin noma da za ta yi gogayya da kowace kwaleji a ko’ina a fadin kasar nan”.
Dan majalisar ya ce, kudurin ya kuma kunshi daga darajar makarantar bayar da horo kan harkokin Noma da ke Daudawa zuwa matakin makarantar gaba da sakandire ta yadda zata rika bayar da shaidar karatu na Diploma da makamantansu a fannin Noma.