Majalisar kolin Musulunci ta tallafa wa marayu a Yobe

Mataimakin Babban Sakataren Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, Farfesa Tijjani El-Miskin ya bukaci masu hannu da shuni da sauran kungiyoyi su rika taimaka wa marayu da marasa karfin da ke cikin al’umma don sauke nauyin da ke kansu da kuma neman yardar Allah.Farfesa Tijjani El-Miskeen ya yi wannan kira ne a garin […]

Majalisar kolin Musulunci ta tallafa wa marayu a Yobe
Majalisar kolin Musulunci ta tallafa wa marayu a Yobe

Mataimakin Babban Sakataren Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta

Najeriya, Farfesa Tijjani El-Miskin ya bukaci masu hannu da shuni da sauran kungiyoyi su rika taimaka wa marayu da marasa karfin da ke cikin al’umma don sauke nauyin da ke kansu da kuma neman yardar Allah.
Farfesa Tijjani El-Miskeen ya yi wannan kira ne a garin Damaturu lokacin da yake rarraba kayayyakin tallafi ga wasu marayu, kayayyakin da majalisar ta samar ga marayun da suka rasa iyaye a sakamakon halin da jihar da yankin ke ciki na tabarbarewar tsaro.
Ya ce, wadannan kayayyakin tallafi da suka hada da kayan abinci da na amfanin yau da kullum majalisar ta samar da su ne ga marayun don rage musu halin matsalolin rayuwar da suke ciki.
Don haka ya roki dukkan masu hannu da shuni da sauran kungiyoyin bada tallafi su rika kokarin amfani da damar da suke da ita don neman Lahira kasancewar kula da maraya babban lamari ne da Allah Yake kira a yi.
Da yake jawabi a wurin bada tallafin Wazirin Gujba Alhaji Gaji Grema yaba wa ya yi da yunkurin Majalisar kolin Addinin Musuluncin na samar da tallafin, inda ya yi kira ga kungiyoyin da ba na gwamnati ba, su shiga sahun irin wadannan ayyuka na ba da tallafi ga marayu da sauran mutanen da suka tagayyara.
Kwamishinan kula da harkokin addinin na Jihar Yobe Alhaji Muhammad Jauro Giwo ya yaba wa majalisar kuma ya gode wa gwamnatin jihar wadda ita ce a kan gaba wajen tallafa wa marayun da matan da suka rasa mazajensu a hare-haren mayaka a jihar.