Majalisar Matasa ta yi tir da taron su Al-Mustapha na Kaduna

Majalisar Matasa ta kasa reshen Jihar Kano ta yi tir tare da nesanta kanta daga taron matasa da Manjo Hamza Al-Mustapha tsohon mai tsaron lafiyar marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha ya gudanar a Kaduna.Wannan yana kunshe a cikin wata takarda da kungiyar ta fitar dauke da sa hannun shugabanta Malam Abdulhadi Zubairu Chula. kungiyar […]

Majalisar Matasa ta yi tir da taron su Al-Mustapha na Kaduna
Majalisar Matasa ta yi tir da taron su Al-Mustapha na Kaduna

Majalisar Matasa ta kasa reshen Jihar Kano ta yi tir tare da nesanta kanta daga taron matasa da Manjo Hamza Al-Mustapha tsohon mai tsaron lafiyar marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha ya gudanar a Kaduna.
Wannan yana kunshe a cikin wata takarda da kungiyar ta fitar dauke da sa hannun shugabanta Malam Abdulhadi Zubairu Chula. kungiyar ta ce ba hannunta a cikin wannan taron kuma ba da yawunta aka yi ba. Ta kara da cewa bincikenta ya nuna cewa wasu masu yunkurin yi wa Arewa zagon kasa wajen ganin ba ta yi tasiri a zaben 2015 ba ne ke kokarin amfani da Manjo Al-Mustapha don cimma wannan buri nasu.
“Ba za mu yarda da wannan yunkuri ba, domin a ganinmu wannan taro akwai lauje cikin nadi a cikinsa saboda haka muke sanar da duk wata kungiya da ke karkashin Majalisar Matasa ta nesanta kanta daga taron. A matsayin wannan majalisa mai wakiltar matasa fiye da miliyan bakwai, mun yi tir da wannan taron domin ba taron da zai haifa wa Arewa da mai ido ba ne,” inji kungiyar.
 A kwanan baya wasu kungiyoyin matasa sun yi irin wannan kira kan wannan taro, daga cikinsu akwai kungiyar Farfado da Matasan Arewa (Northern Youth Rebibal Mobement -NYRM), wadda a wata takarda dauke da sa hannun Kwamared Ahmad Tahir ta yi tir da abin da ta kira alakar Manjo Al-Mustapha da gwamnatin Goodluck abin da ta ce ba zai haifa wa Al-Mustapha abin kirki ba.
Ita ma Majalisar Matasa Arewa (Northern Youth Assembly) reshen Jihar Kano ta fitar da sanarwa dauke da sa hannun shugabanta Malam Surajo Umar Wudil inda ta kalubalanci Manjo Al-Mustapha cewa har yanzu ba ta san a wane matsayi ya gudanar da taron ba.