Majalisar Nasarawa ta amince da sabbin Kwamishinoni 11
Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta amince da nadin sabbin Kwamishinoni 11. Kakakin majalisar jihar Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullah ne ya sanar da hakan bayan da ‘yan majalisar suka tantance takardun sabbin Kwamishinonin. Wadanda aka tantance sun hada da: Hajiya Halima Jabiru, Salisu Abubakar Haske, Phamacist Victor Tella, Musa Suleiman, Hajiya Jamila Sarki, Dakta Roseline Kera, […]
Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta amince da nadin sabbin Kwamishinoni 11.
Kakakin majalisar jihar Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullah ne ya sanar da hakan bayan da ‘yan majalisar suka tantance takardun sabbin Kwamishinonin.
Wadanda aka tantance sun hada da: Hajiya Halima Jabiru, Salisu Abubakar Haske, Phamacist Victor Tella, Musa Suleiman, Hajiya Jamila Sarki, Dakta Roseline Kera, Hajiya Sa’adatu Yahaya, Hudu Yamba, Mary Enwongulu, Dakta Clement Ehemba da kuma Mohamed Bashir Aliyu.