Majalisar Nasarawa ta gayyaci shugabannin gidauniyar tallafa wa ilimi kan rikicin shugabanci
Majalisar ta ce tana son gano abin da ya haddasa rikicin tare da magance matsalar.
Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, ta gayyaci shugaban Hukumar Gudanarwar Gidauniyar Tallafa wa Ilimi ta Jihar, Timothy Anjide, da sauran mambobin hukumar domin su bayyana a gabanta a ranar Litinin, kan rikicin shugabanci.
Shugaban Kwamitin Majalisar mai kula da Asusun Gwamnati da Ilimi, Solomon Yakubu Akwashiki ne, ya bayyana hakan bayan wata ganawa da shugabannin hukumar a harabar majalisar da ke Lafia.
- Matashiya TV ta horar da matasa sama da 3,000 sana’o’i da aikin jarida a Kano
- Uba da ’ya sun mutu a rijiya a Kano
Akwashiki, ya ce majalisar na son gano musabbabin rikicin tare da nemo mafita domin a kawo ƙarshensa.
Ya bayyana cewa shiga tsakanin majalisar na daga cikin ƙoƙarinta na tabbatar da cewa gidauniyar na gudanar da aikinta yadda doka ta tanada.
A nasa jawabin, shugaban hukumar, Timothy Anjide, ya zargi Babban Sakataren gidauniyar da gudanar da harkokin asusun kamar mallakinsa ne.
Ya buƙaci majalisar ta ɗauki matakan da suka dace domin magance matsalolin da suka haddasa rikicin.
Akwashiki, ya tabbatar da cewa majalisar za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin gidauniyar ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa ƙa’idar da aka kafa ta.
Majalisar ta kuma ce zaman da za a yi ranar 27 ga watan Yuli zai haɗa shugabannin hukumar da Babban Sakataren domin su bayyana matsayinsu a fili, da nufin kawo ƙarshen rikicin.