Majalisar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Fubara
Tsohon Gwamna Wike, ya ce babu abin da zai faru idan Majalisar Ribas ta tsige Fubara.

Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Similanayi Fubara daga muƙaminsa.
Hakan na ƙunshe cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa mai cike da ƙorafi da majalisar ta fitar, inda take shirin tsige Gwamnan tare da mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu.
A cikin wasiƙar wadda take kafa hujja ta tanadin da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya yi, ’yan majalisar sun zargin Gwamna Fubara da kashe kuɗaɗen jama’a ba bisa ƙa’ida ba.
Haka kuma, wasiƙar ta ce Gwamna Fubara ya hana majalisar gudanar da aikinta, da kuma naɗa mutane a muƙaman gwamnati ba tare da tantancewa ba.
Kazalika, tana tuhumar Gwamnan da ƙin biyan albashi da wasu alawus alawus da aka ware wa majalisar ciki har da dakatar da albashin Sakataren Majalisar, Emeka Amadi.
A bayan nan ne tsohon Gwamnan Ribas kuma Ministan Abuja mai ci, Nyesom Wike, ya ce ba zai hana majalisar sauke nauyin da rataya a wuyanta ba wajen tsige Gwamna Fubara.
A wata hira da manema labarai da ya gabatar ranar Laraba a Abuja, Mista Wike ya ce ’yan majalisar ba su yi laifi ba idan suka yanke shawarar tsige Fubara, saboda ya aikata laifukan da suka cancanci a tsige shi, ciki kuwa har da riƙe musu albashi na tsawon watanni.
Aminiya ta ruwaito cewa, tun bayan ’yan watanni da zama Gwamnan Ribas, aka sa zare tsakanin Fubara da Wike, inda har kawo yanzu rikicin siyasa a tsakanin ɓangarorin biyu ke daɗa ƙamari.