Majalisar Sakkwato ta amince da kudurin dokar Hukumar Hisbah

Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta amince da kudurin dokar kafa Hukumar Hisbah ta Jihar. Zaman Majalisar ta ranar Alhamis ta amince da dokar ce bayan karbar rahoton Kwamitinta na Harkokin Addini da Shari’a da Hakkoki Dan Adam. Yadda ake sayen burodi, haka muke sayen makamai —Daudawa Sunayen dalibai da malaman da aka sace a Makarantar […]

Majalisar Sakkwato ta amince da kudurin dokar Hukumar Hisbah

Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta amince da kudurin dokar kafa Hukumar Hisbah ta Jihar.

Zaman Majalisar ta ranar Alhamis ta amince da dokar ce bayan karbar rahoton Kwamitinta na Harkokin Addini da Shari’a da Hakkoki Dan Adam.

Da yake gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin, Alhaji Abubakar Yabo ya ce Kwamitin ya yi tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki kafin ta cimma matsayar.

Zauran Majalisar ya amince da kudirin kafa Hukumar Hisbar ce bayan Shugabanta Aminu Achida ya gabatar da batun a zaman nasu.