Majalisar Sakkwato ta kafa dokar hana tsadar aure
Za a kawo karshen tsada da almubazzarancin da jama’a ke yi a bikin aure a jihar.
Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ta sanya hannu kan wani kudirin dokar da ke sanya ido kan tsada da almubazzarancin da jama’a ke yi a bikin aure a jihar.
Kudirin wanda Alhaji Abubakar Shehu na jam’iyyar APC da Faruk Balle na jam’iyyar PDP suka gabatar, sai da aka fara gabatar da shi ga Kwamitin Kula da Al’amurran Addini a majalisar.
- ’Yan mata 15 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Sakkwato
- An kama tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan
Shehu wanda shi ne shugaban kwamitin, ya gabatar da rahotonsu a wani zaman farko na ‘yan majalisar kuma daukacinsu suka amince ya zama doka.
Kudirin dokar na bukatar sanya ido kan almubazzarancin kudi da ake yi a yayin bikin aure da taron suna da kaciya da sauran bukukuwa a sassan jihar.
Bayan wata muhawara a zaman na farko da Mataimakin Shugaban Majalisar ya jagoranta, Alhaji Abubakar Magaji, kudirin dokar ya samu amincewar ’yan majalisar.
RFI