Majalisar sarakuna ta nemi a zauna lafiya a Jihar Nasarawa
Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiyar Jihar Nasarawa, wanda shi ne kuma Sarkin Lafiya, Alhaji Isah Mustapha Agwai ya bukaci al’ummar jihar baki daya, musamman wadanda ke fada da junansu da su rungumi zaman lafiya don ci gaban jihar.Ya bayyana haka ne a wajen wata addu’a ta musamman da kuma taron neman zaman lafiya a tsakanin kabilu […]
Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiyar Jihar Nasarawa, wanda shi ne kuma Sarkin Lafiya, Alhaji Isah Mustapha Agwai ya bukaci al’ummar jihar baki daya, musamman wadanda ke fada da junansu da su rungumi zaman lafiya don ci gaban jihar.
Ya bayyana haka ne a wajen wata addu’a ta musamman da kuma taron neman zaman lafiya a tsakanin kabilu daban-daban da ke jihar, wanda majalisar ta shirya a fadar mai martaba sarkin Lafiya a karshen makon da ya gabata.
Basaraken gargajiyan ya ce addu’ar ta musamman ta zame dole kuma tana da mahimmanci sosai ganin yadda a yanzu kusan dukkan sassan jihar na fuskantar rigingimu musamman na kabilanci. Ya ce zaman lafiya ita ce hanya daya tilo da za a iya samun dawwamammen cigaba a jihar baki daya. Don haka ya bukaci al’ummar jihar da su zauna lafiya da junansu a koyaushe, ba tare da nuna bambancin addini, siyasa ko kabilanci ba.
Game da harin da wasu mayaka suka kai garin Lafiya, da ya jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma da dama, basaraken ya nuna bakin cikinsa game da haka; inda ya kwatanta lamarin a matsayin abin assha. Ya kara da cewa duk da cewa Lafiya ce fadar mulkin jihar da kowanne kabila ke zuwa, musamman a lokacin tashin-tashina amma sai ya kasance ita ma ta samu nata kason rikicin na baya-bayan nan. Ya ci gaba da bayyana cewa, a nata bangaren, masarautar Lafiya da majalisar sarakunan gargajiya na jihar, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fadakar da al’ummar jihar baki daya game da bukatar tabbatar da zaman lafiya a yunkunansu, don a samu zaman lafiya mai dorewa a jihar baki daya.
Idan ba a manta ba, a ’yan kwanakin nan ne sabon rikici ya barke tsakanin mayakan kabilar Eggon da aka fi sani da Ombatse da na Kambari a Lafiya, inda aka kashe rayuka aka kuma lalata dukiyoyin miliyoyin Naira. Hakan ya sa majalisar sarakunan ta shirya wannan taro.