Majalisar Sardaunan Matasa za ta fito da ’yan Arewa daga gidan yari a Legas

Majalisar Sardaunan Matasan Sakkwato, ta fara tuntubar lauyoyi da za su taimaka mata wajen gano ’yan Arewa da ke tsare, ba tare da aikata laifin komai ba, a gidajen yari da ke Legas domin fito da su. Majalisar ta dauki wannan mataki ne saboda lura da ta yi jami’an tsaro a Legas, sukan kama mutane, […]

Majalisar Sardaunan Matasa za ta fito da ’yan Arewa daga gidan yari a Legas
Majalisar Sardaunan Matasa za ta fito da ’yan Arewa daga gidan yari a Legas

Sardaunan matasan Sakkwato, Alhaji Mujitaba Isa Helele yana ganawa da ’yan jaridaMajalisar Sardaunan Matasan Sakkwato, ta fara tuntubar lauyoyi da za su taimaka mata wajen gano ’yan Arewa da ke tsare, ba tare da aikata laifin komai ba, a gidajen yari da ke Legas domin fito da su. Majalisar ta dauki wannan mataki ne saboda lura da ta yi jami’an tsaro a Legas, sukan kama mutane, musamman ’yan Arewa da ke gudanar da kananan sana’o’i, suna tsare su a gidajen yari, ba tare da an gurfanar da su gaban kotu ba, domin babu laifin da za a tuhume su da shi.
Sardaunan Matasan Sakkwato, Alhaji Mujitaba Isa Helele, shi ne ya fadi haka cikin hirarsu da wakilinmu jim kadan bayan kammala wani taro da ’yan majalisarsa suka halarta a ofishinsu da ke Marine Beach, Apapa a Legas. Ya ce, “tabbatattun bayanai da muka samu sun nuna cewa, akwai mutanenmu da yawa da jami’an tsaro suka kama su, ba tare da aikata laifi ba, kuma ake tsare su a gidajen yari. Majalisarmu ta fara tuntubar wasu lauyoyi da za ta yi amfani da su wajen fito da irin wadannan mutane. Su ma gidajen marayu suna cikin jerin wuraren da za mu ziyarta domin tallafa musu”.
Alhaji Mujitaba ya yi fatar masu hannu da shuni su yi amfani da dukiyarsu wajen ceto irin wadannan ’yan uwa nasu da ake tsarewa, kamar yadda su suke yi a bangarensu.
Ya ce a Jihar Sakkwato, majalisar ta ziyarci asibitin Maryam Abacha ta bayar da tallafi ga kananan yara da suka kamu da cutuka daban-daban da mata masu yoyon fitsari.
A karshe Sardaunan ya yi kira ga ’yan uwa da ke zaune a Legas da sauran jihohin Kudu su kyautata zamantakewarsu da sauran jama’a, su girmama doka da oda, sannan su rika yi wa magabata fatan alheri, musamman saboda fafutukar da suke yi na kwato musu ’yanci.