Majalisar Sarkin Hausawan Ogere tana kokarin sama wa jama’arta ’yancin walwala

Sarkin Hausawan Ogere a Jihar Ogun, Alhaji Abdullahi Abubakar Saminaka ya bayyana irin tsayuwar dakan da masarautarsa take yi wajen  fafutukar samar da ’yancin walwala ga al’ummarta, wadda take nuna wa muhimmancin girmama dokokin kasa da kyautata zamantakewa tsakaninta da jama’ar gari. “Muna fadakar da al’ummar Hausawa kan muhimmancin girmama dokoki da kuma kokarin kai […]

Majalisar Sarkin Hausawan Ogere tana kokarin sama wa jama’arta ’yancin walwala

Sarkin Hausawan Ogere a Jihar Ogun, Alhaji Abdullahi Abubakar Saminaka ya bayyana irin tsayuwar dakan da masarautarsa take yi wajen  fafutukar samar da ’yancin walwala ga al’ummarta, wadda take nuna wa muhimmancin girmama dokokin kasa da kyautata zamantakewa tsakaninta da jama’ar gari.
“Muna fadakar da al’ummar Hausawa kan muhimmancin girmama dokoki da kuma kokarin kai koke-kokensu ga na gaba da su ko jami’an tsaro domin magance matsalolin zamantakewa da akan samu a tsakaninsu da jama’a.” Inji shi.
Sarkin Hausawan ya fadi haka ne a hirarsu da Aminiya, jim kadan bayan wani zama na musamman da ya yi da ’yan majalisarsa. A zaman an tattauna kisan gillar da barayi suka yi wa wasu Hausawa masu sana’ar sayen babur suna sayarwa, wanda har zuwa lokacin ba a gano gawar daya daga cikinsu ba, alhali daya gawar an gano ta, bayan an yanke wani sashe na jikinta.
Sarkin ya ce, “Hamzarta sanar da ’yan sanda ya kai ga kama wasu daga cikin barayin har da bokan da aka kai masa sashen jiki ya yi tsafi, suna hannun ’yan sanda, suna ci gaba da bincike. Mutumin da ya kira mutanen su je su sayi babur ya tsere ba a gano maboyarsa ba tukuna. Amma ’yan sanda, musamman AC na Shagamu da DPO na Ishara sun yi namijin kokari kuma sun ba mu tabbacin cewa za su yi duk abin da suke iyawa wajen gano mutumin da ya jagoranci kulla makircin kisan abokan huldarsa.”
Da yake amsa wata tambaya, Sarkin Hausawan ya ce yana samun kyakkyawan hadin kai a tsakaninsa da mataimakansa, wadanda ya bayyana, “Suna gudanar da ayyukansu tsakani da Allah ba domin neman abun duniya ba sai domin kishin ’yan uwansu. Ita ma kungiyar Sarakunan Hausawan Jihar Ogun da muke yin taro a kowace Lahadin karshen mako, muna tattaunawa ne a kan batutuwan da suka shafi rayuwar mutanenmu a wannan jiha kuma tun daga lokacin kafa kungiyar zuwa yanzu, mahukunta sun fara gayyatarmu domin zaman bullo da hanyoyin kyautata zama lafiya da ci gaban jama’a. Yanzu haka ’ya’yanmu sun fara cin moriyar guraben karatu har zuwa Jami’a, wanda ba sa samun irin haka a baya”.  
Game da cunkoson manyan motoci a garin na Ogere, sarkin ya ce gwamnati ta girke jami’an tsaro na soja da ’yan sanda, dare da rana don daidaita al’amura sosai, lamarin da, “Ya taimaka wajen fatattakar barayin da suka dame mu a can baya. Kuma muna godiya ga direbobi da suke ba da hadin kai wajen ajiye motoci a wuraren da aka kebe musu.” Inji shi.