Majalisar Sarkin Musulmi za ta gina jami’ar mata zalla

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce shirye-shirye sun kammala don gina jami’ar mata zalla da majalisarsa ke yi..Sarkin Musulmin ya furta haka ne a ranar Asabar da ta gabata wurin bikin kaddamar da littattafai uku da Diraktar Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato Dokta Sadiya Umar ta […]

Majalisar Sarkin Musulmi za ta gina jami’ar mata zalla

Handmade Software, Inc. Image Alchemy v1.14

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya ce shirye-shirye sun kammala don gina jami’ar mata zalla da majalisarsa ke yi..
Sarkin Musulmin ya furta haka ne a ranar Asabar da ta gabata wurin bikin kaddamar da littattafai uku da Diraktar Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato Dokta Sadiya Umar ta rubuta wanda aka gudanar a dakin taro na Makarantar Fasaha da kere-kere ta Jihar Sakkwato.
Ya ce jami’ar za ta mayar da hankali wurin koyar da mata Musulmi sha’anin kiwon lafiya saboda Musulmi mata a kasar nan na fuskatar kalubale in suka tafi asibitoci kan wata matsala da ta shafe su. Ya ce “Sai ka ga maza ne za su kula da su wannan ya kara yi mana azama muka ga lallai ba makawa sai mun gina wannan jami’ar don taimaka wa ’ya’ya mata a kasar nan baki daya,” inji shi.
Sarkin Musulmin ya ce majalisarsa za ta ci gaba da taimaka wa duk wani shiri na mata da zai kawo ci gaba, domin mata a kasar nan suna da kaifin basira musamman na yankin Arewa “Malama Sadiya ta nuna mata na karatu da karantarwa a wannan yankin domin rubuta wadannnan littattafai uku suna kara nuna mana yadda ilimin mata ya samu gindin zama a cikinmu. Karantar da mata kamar karantar da kasa ce gaba daya, nan gaba kadan za mu fito wa al’umma yadda tsarin jami’ar mata zai kasance. A yanzu dai wasu mutane ne masu amana da dattako muka ba aikin kuma ana samun gagarumar nasara,” cewar Mai alfarma Sarkin Musulmi.
Ya bukaci Jami’ar Usman dan Fodiyo ta fito da wani sashi a jami’ar da za a rika bincike kan Daular Usmaniyya.
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Wamakko ya yaba wa marubuciyar inda ya ce gwamnati za ta cigaba da taimaka wa karatun mata a jihar.Gwamnan wanda Kwamishinan A’lamurran Addini Alhaji Tukur Alkali ya wakilta ya ba da gudunmuwar Naira miliyan 5 da gwamnatin Sakkwato ta sayi littaattfan guda uku.
Uwar gidan Mataimakiyar Shugaban kasa Hajiya Amina Namadi Sambo kuwa ta yi kira ga gwamnonin Arewa da shugabannin kananan hukumomi ne kan su sayi littattafan domin amfanin yara a makarantunsu.
Ta jinjina wa marubuciyar kan wannan hobbasa da ta yi domin kawo wa ilimin matan kasar nan ci gaba.
A wurin Kaddamar da littattafan uku masu suna MODIBBO KILO da ’YAN TARUN NANA ASAMA’U da FASAHAR ’YAN MAZAN-JIYA, an tara fiye da Naira miliyan 20.
A wurin bikin Sarkin Musulmi ya nada marubuciyyar Malama Sadiya sarautar ‘Uwar ‘Yan Taru.’