Majalisar Shura ta yi taro da kungiyoyin Musulunci don yakar luwadi da madigo
Majalisar Shura da ta kunshi dukkan kungiyoyin addinin Musulunci na Jihar Bauchi ta yi taro domin wayar da kan jama’a da shugabannin kungiyoyin game da yadda za a dakile mummunar dabi’ar aikata luwadi da madigo a makarantu da kowane sashi na jihar.Hakimin Bauchi Alhaji Nuru Adamu Jumba wanda ya jagoranci taron a dakin taro na […]

Majalisar Shura da ta kunshi dukkan kungiyoyin addinin Musulunci na Jihar Bauchi ta yi taro domin wayar da kan jama’a da shugabannin kungiyoyin game da yadda za a dakile mummunar dabi’ar aikata luwadi da madigo a makarantu da kowane sashi na jihar.
Hakimin Bauchi Alhaji Nuru Adamu Jumba wanda ya jagoranci taron a dakin taro na Babban Masallacin Bauchi a ranar Lahadin da ta gabata ya nemi iyaye su tashi tsaye wajen sanya ido ga ’ya’yansu a gida da waje.
Ya nuna takaici game da yadda muguwar dabi’ar nan ta luwadi da madigo ke yawaita a cikin jama’a kamar dalibai da matasa da ’yan mata da malamai da masu rike da sarautun gargajiya, inda ya bukaci hukuma ta tashi tsaye don daukar mataki a kai su kuma iyaye su sanya ido kan halin da ’ya’yansu ke ciki.
Babban bako mai wa’azi Ustaz Albashir Tahir Jahun ya bayyana illoli da hadari da hukunce-hukuncen da ke tattare da aikata luwadi da madigo a cikin al’umma, ya nemi a sanya ido a makarantu saboda wasu yaran na koya ne a wurin neman ilimi, inda ake kai samun wasu malamai na aikata wannan fasadi da dalibai. Kuma ya bukaci a tsananta hukunci ga masu aikata wannan mugun aiki.
Shugaban Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi Malam Mustapha Baba Ilela a laccar da ya gabatar, ya yi bayani ne kan irin nauyin da ya hau kan kowa na hana yaduwar wannan laifi, inda ya ja hankalin malamai da limamai da shugabannin makarantu da sarakuna da masu unguwanni da sauran hukumomi su tabbatar sun sa ido domin dakile abin da ke faruwa na fasadin luwadi da madigo a cikin al’umma.
Kwamishinan Hisbah na Jihar Bauchi Malam Abdurrahman Ahmad Ibrahim Khalil a ta’alikin da ya yi kan laccar da malamai suka gabatar ya ja hankalin jama’a ne kan su sanya ido domin kawo karshen wannan matsala, musamman ganin yadda ake samun malaman addini da na boko na aikata wannan fasadi da daliban da aka ba su amana. Ya roki iyaye su zama masu kiwo a kan ’ya’yansu don a samu dakile wannan mummunan aiki.