Majalisar Spain ta amince da kudirin kafa kasar Falasdinu
A ranar Talatar da ta gabata ne Majalisar Dokokin kasar Spain ta amince da kudirin amincewa da kafa kasar Falasdinu da gagarumin rinjaye. A lokacin zaman ’yan majalisar su 319 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudirin, yayin da biyu suka yi adawa, sai kuma guda da ya kaurace wa zaman.kudirin wanda ’yan adawar kasar […]
A ranar Talatar da ta gabata ne Majalisar Dokokin kasar Spain ta amince da kudirin amincewa da kafa kasar Falasdinu da gagarumin rinjaye.
A lokacin zaman ’yan majalisar su 319 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudirin, yayin da biyu suka yi adawa, sai kuma guda da ya kaurace wa zaman.
kudirin wanda ’yan adawar kasar suka bukaci gwamnatin kasar da ta amince da kafa kasar Falasdinu kamar yadda wasu kasashen Tarayyar Turai suka fara yi.
Har ila yau, kudirin wanda ya yi kama da wanda Majalisar Dokokin Birtaniya da ta Jamhuriyar Ireland, ya samu goyon bayan duka kungiyoyin siyasar kasar da ke majalisar wakilan kasar. Kuma duka wadannan na zuwa ne a daidai lokacin da a watan jiyan sabuwar gwamnatin kasar Sweden take shirin amincewa da Falasdinun a matsayin kasa.
Kodayake Ministan Harkokin Wajen kasar Spain din Jose Manuel Garcia-Margallo wanda kuma shi ne jami’in gwamnatin kasar daya tilo da ya halarci zaman majalisar, ya ce gwmnatin kasar a shirye take don ganin an samu sulhu tsakanin bangarorin biyu saboda “wanzuwar zaman lafiya da ci gaba a yankin Gabas-ta-Tsakiya wanda ya dade yana fama da rikici,” inji shi. Daga karshe ya bukaci Tarayyar Turai da ta hada kai wajen lalubo hanyar maganin rikicin.