Majalisar ta bukaci EFCC ta binciki sayo motoci masu sulke da Gwamna Ngilari ya yi
Majalisar Dokokin Jihar Adamawa ta bukaci Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) ta yi bincike a kan motoci kirar Hilud guda 50 da kuma motoci biyu masu sulke da Gwamnan Jihar Bala James Ngilari ya sayo kan Naira miliyan 590 a cikin wata shida da ya yi a karagar mulki. Majalisar […]
Majalisar Dokokin Jihar Adamawa ta bukaci Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) ta yi bincike a kan motoci kirar Hilud guda 50 da kuma motoci biyu masu sulke da Gwamnan Jihar Bala James Ngilari ya sayo kan Naira miliyan 590 a cikin wata shida da ya yi a karagar mulki.
Majalisar ta kuma bukaci gwamnatin jihar ta sake duba korar Darakta Janar na Jihar mai binciken abubuwan da jihar ke saya, Mallam Bello Umar wanda aka kore shi domin ya ce yadda gwamnatin ta sayo motocin ba a kan tsari yake ba.
Shugaban Majalisar Alhaji Ahmadu Fintiri ya bai wa Malam Bello Umar lambar yabo domin yadda ya tambayi gwamnatin jihar kan yadda ta sayo wadannan motoci ba a bisa tsari ba.
Majalisar ta dauki wadannan matakai ne a yayin zaman tattaunawar da ta yi a karkashin Mataimakin Shugaban Majalisar Mista Kwamoti Laori inda ta ce an kori Daraktar Janar din ne saboda tambayar gwamnati kan yadda ta sayo motocin Hilud 50 a kan Naira miliyan 400 da motoci kirar jeep samfurin Ledus masu sulke guda biyu a kan Naira miliyan 190.
Laori ya ce motoci masu sulke da Gwamna Ngilari ya sayo ba sababbi ba ne kuma ana sayar da kowace daya a kan Naira miliyan 35 ne a ksauwa.
Laori ya kara da cewa korar Daraktar Janar din da aka yi ta hanyar wasika da sakatare ya ba shi ba a kan tsari yake ba, domin ba za a kore shi ba, sai ’yan majalisa sun zauna sun tattauna da manyan ’yan majalisa.